Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ɗaga darajar Abdul’aziz Abdul’aziz daga matsayin Mataimaki na Musamman zuwa Babban Mataimaki na Musamman kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a.
Naɗin, wanda aka sanar a hukumance, ya nuna gamsuwa da irin ƙwazo, sadaukarwa da kuma gudunmawar da Abdul’aziz ya bayar wajen gudanar da harkokin yaɗa labarai da sadarwa a Fadar Shugaban Ƙasa.
An bayyana ƙarin girman a matsayin wata alama ta amincewa da ƙwarewarsa da kuma muhimmiyar rawar da yake takawa wajen isar da manufofi da ayyukan gwamnati ga al’umma.
Da yake martani kan sabon naɗin, Abdul’aziz Abdul’aziz ya ce karin girman ya ƙara masa nauyi da alhakin da ke kansa.
“Wannan amana tana buƙatar ƙarin ƙwazo, jajircewa da sadaukarwa. Ba zan yi ƙasa a guiwa ba wajen sauke nauyin da aka ɗora mini,” in ji shi.
Ya kuma miƙa godiyarsa ga Shugaba Tinubu bisa ci gaba da nuna masa amincewa da goyon baya, yana mai cewa wannan ƙarin girma zai ƙara masa ƙaimi wajen yi wa ƙasa hidima.
Haka zalika, ya yaba wa shugabanninsa, abokan aikinsa da sauran masu ruwa da tsaki a harkar sadarwa bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen nasarorin da ya samu.
Abdul’aziz ya tabbatar da cewa ya karɓi takardar tabbatar da sabon naɗin nasa, wanda ya fara aiki daga ranar 23 ga Afrilu, 2026, bisa sabon tsarin aikin da Shugaban Ƙasa ya amince da shi.







