‘Yan Kasuwar Larabar Mata Sun Jajanta Wa ’Yan Kasuwar Singa A Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Shugaban Kasuwar Larabar Mata, Alhaji Umar Alasan, ya jajanta wa ’yan kasuwar Singa bisa gobarar da ta tashi ta shafe su, inda ya bayyana lamarin a matsayin babbar masifa da ta shafi kowa da kowa, la’akari da cewa Kano cibiya ce ta kasuwanci a ƙasar nan.

Ya yi kira ga shugabanni a matakin jiha, ƙasa da kuma ƙananan hukumomi da su haɗa kai da masu hannu da shuni domin taimaka wa waɗanda gobarar ta shafa, tare da ɗaukar matakan da suka dace wajen bincike da gyara duk wasu abubuwan da ke haddasa gobara irin wannan, domin kauce wa maimaituwarta nan gaba.

Haka kuma, ya ƙara da yin kira ga ’yan kasuwa, kasancewar ana gab da shiga watan Azumin Ramadan, da su sassauta farashin kayayyakin masarufi domin al’umma su samu sauƙin saye, su rayu cikin walwala tare da gudanar da ibada cikin kwanciyar hankali da natsuwa.

Alhaji Umar Alasan ya kuma jaddada muhimmancin taka-tsantsan da kulawa a kasuwanni domin kauce wa haɗurra, yana mai kira ga kowa da kowa ya sauke haƙƙin Allah da ke kansa, ya tausaya wa jama’a, tare da fatan Allah Ya kare dukiyoyin ’yan kasuwa daga iftila’i.

Shugaban ya ce Allah Ya sanya albarka a Kasuwar Larabar Mata, wadda al’umma daga Kudu da Arewa, Gabas da Yamma ke shigowa cikinta, kuma tana ci gaba da bunƙasa.

Ya bayyana cewa kasuwar ta daɗe tana wanzuwa tun zamanin Turawa, lokacin da ake zuwa ba da magani ga masu cutar kuturta, inda daga bisani ta bunƙasa har ta zama babbar kasuwa.

Ya ƙara da cewa asalin sunan “Larabar Mata” ya samo ne daga yadda mata dattijai da ’yan mata ke zuwa kasuwar a wancan lokaci suna sayar da kayayyakin gargajiya a ranakun da ake gudanar da ayyuka, wanda hakan ya sa sunan ya tabbata har zuwa yau.

Alhaji Umar Alasan ya ce lokacin da suka karɓi shugabancin kasuwar sun tarar da wasu ƙalubale, amma da taimakon Allah suka ɗauki matakai suka inganta tsaro, suka ƙarfafa fahimtar juna tsakanin ’yan kasuwa, tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro na ’yan sanda, masu sa kai da shugabannin kasuwa domin tabbatar da zaman lafiya.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo