Alakanta Zargin ɓatan Dadiyata da El-Rufa’i da Ganduje: Amnesty International Ta Buƙaci A Yi Cikakken Bincike

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Nijeriya da su zurfafa bincike kan ɓatan fitaccen ɗan gwagwarmaya Idris Abubakar da aka fi sani da Dadiyata domin gano gaskiyar abin da ya faru.

Ƙungiyar ta bayyana cewa zargin da tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El‑Rufai, ya yi na cewa gwamnatin tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, na da masaniya kan ɓatan Dadiyata lamari ne mai girma da ke buƙatar cikakken bincike na gaskiya.

El-Rufa’i ya bayyana cewa bai san inda Dadiyata yake ba, yana mai cewa kasancewar Dadiyata na adawa da gwamnatin Ganduje kuma ana danganta shi da tafiyar Kwankwasiyya, a lokacin mulkin Ganduje ne aka kai hari gidansa da ke Kaduna aka kuma ɗauke shi.

Dangane da wannan zargi, tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na gwamnatin Kano, Muhammad Garba, ya musanta alaƙanta Ganduje da lamarin, yana mai cewa babu ƙanshin gaskiya a cikin zargin, tare da buƙatar a gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru.

A ranar 2 ga Agusta, 2019 ne wasu da ba a san ko su waye ba suka je gidan Dadiyata da ke Kaduna suka ɗauke shi, kuma tun daga lokacin babu wani bayani tabbatacce kan inda yake.

  • Related Posts

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Hon Alhaji Bashir Abubakar Galadima, hadimin Gwamnan jihar Kano a ma’aikatar kananan hukumomi, ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka kammala gyare-gyaren kasafin kudin shekarar 2027…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength