Ƙaramar Hukumar Fagge Ta Raba Takardun Shaidar Ɗaukar Aiki Na Dindindin Ga Malaman Makaranta, Tare Da Biya Ma’ikatan Wucin Gadi

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Shugaban Karamar Hukumar Fagge, Hon. Salisu Masu ya jagoranci taron raba takardun aikin malanta ina dindindin na SUBEB da na wucin gadi na BESDA, tare da biyan albashin ma’aikatan wucin gadi da suka hada na Asibitoci 14.na yankin da masu haqan Kaburbura da masu gadi na Karamar Hukumar, a da aka gudanar a harabar a sakatariyar Karamar Hukumar ranar Juma’a.

A jawabin sa, Hon.Salisu Masu ya bayyana cewa taron ya biyo bayan umarnin Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, na daukar kaddamar da 8000 a matakin jiha da suma suke bayar da shaidar daukar malaman a matakin kananan hukumomi bayan kaddamar da na Jiha.

Ya ce an ba da takardun aikin malanta i na dindindin ga mutum. 90 a karkashin SUBEB, yayin da sama da 100 kuma suka samu na wucin gadi karkashin shirin BESDA.

Kuma mun yi musu alkawarin cewa nan gaba idan aka samu dama za mu mayar da su na dindindin, inji shi.

Shugaban ya taya sabbin ma’aikatan murna, sannan ya ja hankalinsu da suyi aiki cikin gaskiya, amana da kishi.

Hon. Salisu Masu ya kuma yabawa ma’aikatan wucin gadi na Asibitoci bisa hakuri da sadaukarwa da suka nuna a lokacin da aka samu tsaiko wajen biyan albashinsu.

Hon. Salisu Masu ya godewa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ayyukan ci gaba da yake kawo wa Karamar Hukumar Fagge.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Fagge da su ci gaba da baiwa Jam’iyyar APC hadin kai da goyon baya, ta yadda za a zabi yan takararta daga sama har kasa a zaben 2027.

A jawabinsa Shugaban Kwamitin Ma’aikatan wucin gadi na Asibitoci, Masallatai da masu haka kaburbura, kuma Kansilan Mazabar Fagge C, Hon. Sunusi Sharif Kantoma. ya bayyana cewa shugabanna fagge ne ya kafa kwamitin tare da kara albashin ma’aikatan wucin gadi daga N1,900 zuwa N10,000.

Yace da farko shugaban.karamar hukumar ya so ma ya mayar da albashin N20,000, amma saboda halin da ake ciki sai muka daidaita kan N10,000. Yanzu haka suna da ma’aikata 248 da za su biya su albashin watanni biyu da suka gabata, nan gaba kuma za su ci gaba da biyansu,” inji Kantoma.

Ya tabbatar wa ma’aikatan wucin gadin cewa idan aka samu dama ta daukar ma’aikata na dindin, za a ba su fifiko.

A nata jawabin a madadin Shugaban SUBEB, Daraktar Shiyya ta SUBEB, Hajiya Zainab Usman Namadi, ta yabawa Hon. Masu bisa kulawa da yake ba malamai.

Ta ja hankalin malamai da aka dauka da su rika ganin aikin koyarwa a matsayin sadaukarwa.

“A aikin koyarwa ba inda Allah ba zai kai ka ba. Ni ma daga koyarwa na fara, har na kai matsayin Daraktar Shiyya. Hatta Shugaban Karamar Hukumar Fagge ma ya taba yin malanta . Don haka ku yi aiki tukuru cikin rikon amana,” ta shawarci ma’aikatan dindindin na SUBEB da na BESDA.


Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati ciki har da Sakataren Mulki na Karamar Hukumar Fagge da sauran masu ruwa da tsaki.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo