ƘARAMAR SALLAH: GWAMNAN ZAMFARA YA TAYA MUSULMI MURNA

ƘARAMAR SALLAH: GWAMNAN ZAMFARA YA TAYA MUSULMI MURNA, TARE DA YIN KIRA GARE SU SU ZAFAFA WURIN YIN ADDU’AR SAMUN ZAMAN LAFIYA

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya taya ɗaukacin al’ummar Musulmi murnar zagayowar ranar ƙaramar Sallah, tare da yin kiran a ƙara ƙaimi wajen addu’o’in samun zaman lafiya a Zamfara da Nijeriya baki ɗaya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce watan Ramadan ya ba da damar yin addu’ar neman taimakon Allah kan matsalar tsaron ƙasar nan.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ya kamata al’ummar Musulmi su ci gaba da nuna kyawawan ɗabi’u da halayyen ƙwarai har bayan watan Ramadan.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Bikin ƙaramar sallah wani lokaci ne na farin ciki, domin yana nuna nasarar kammala azumi da kuma kusanci da Ubangiji da aka samu a cikin watan Ramadan mai alfarma.

“A ranar Idi, Musulmi suna nuna godiya ga lafiya da damar da ya ba su na sauke nauyin da aka ɗora musu na azumi.

“Ya kamata mu yi amfani da wannan lokacin biki don inganta zaman lafiya da nuna soyayya ga juna.

“Don magance matsalolin tsaro da Nijeriya ke fuskanta, dole ne mu sa ido ga juna, mu tsaya tsayin-daka kan addu’o’in mu, sannan mu mara wa ƙoƙarin gwamnati baya na kawo ƙarshen duk wasu masu aikata muggan laifuka.

“Ina taya ɗaukacin al’ummar Musulmin Zamfara da Nijeriya da ma duniya baki ɗaya murna. Da fatan za a yi bukukuwan Sallah lafiya kuma cikin ƙoshin lafiya,” in ji sanarwar.

Related Posts

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum