Daga Ibrahim Muhammad
“Ina farin ciki da ganin yadda yaranmu suka yi sauka ta haddar Alqur’ani mai girma da godiya ga Allah bisa ƙoƙari da jajircewa da muka yi muka tabbatar sun yi karatun.”
Alhaji Ali Sani da aka fi sani da Ali Nagarta, shugaban kamfanin Nagarta ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da ‘yan jarida bayan kammala taron saukar ɗalibai a makarantar Riyadu a Tangaza.
Cikin murna da tsananin farin ciki da ya sa shi har ya fitar da hawaye ya ce, “Jajircewar da iyayen yara suka yi wajen bai wa ‘ya’ya tarbiyya tun daga gida, don ɗa in ka ba shi tarbiyya zai yi abin da kake so sannan kuma da bada kulawa sosai wajen sauke haƙƙoƙin makaranta.”
Ya yi nuni da cewa duk irin hidima da sukewa makarantar sun gamsu matuƙa da karatu da malamanta suke koyawa ɗalibai suna sauke nauyi na koyar da ɗalibai karatu mai inganci shi ne ma ya sa yanzu suka zo suka shaidi bikin saukar karatun Alƙur’ani da ‘ya’yansu suka yi. “Wannan hadda abin farin ciki a gare mu,” in ji shi.
Alhaji Ali Nagarta ya ƙara da cewa, wannan rana ta farin ciki ce a gare shi da ba zai misaltu ba. “Muna gode wa Allah bisa wannan ni’ima a gare mu a ce ɗan da ka haifa ko kai ba ka haddace Alƙur’ani ba, shi kuma ga shi ya zo ya maye gurbinka. Don haka babu abin da za ka ce sai godiya ga Allah,” ya ƙarƙare.








