Ya Kamata Makarantun Islamiyya Su Riƙa Gayyatar Shugabanni Walimar Sauka -Majidadin Ɗan Malikin Zannan Kazaure

Daga Ibrahim Muhammad

Hon. Sulaiman Isah Majidadin Ɗan Malikin Zannan Kazaure, kuma mai bai wa shugaban ƙaramar hukumar Ungogo shawara a harkar noma da kiwo, ya yi kira ga masu gudanar da makarantun Islamiyya su riƙa gayyatar masu muƙamai na siyasa da sauran shugabanni wajen walimar sauka da suke yi, domin hakan zai sa su ga irin buƙatun makarantun don su riƙa tallafawa cigabansu.

Ya ce su a matsayinsu na iyaye sun zo walima ne don shaidar saukar Alƙur’ani mai girma na ‘ya’yansu da suka yi musaffa da tilawa, wasu sun haddace izu 60, wasu 30. Abin alfahari ne da jin daɗi mutum a ce ya samu ɗansa yana cikin wanda ya haddace Alƙur’ani.

“Dan haka a matsayina na uba, ina jan hankalin makarantu su riƙa gayyatar manyan mutane, musamman masu maƙaman siyasa tun daga zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Ungogo da ‘yan majalisu na tarayya da na jiha, domin ta nan ne idan mutum ya zo kusa da kai zai ga ta inda za su kawo gudunmawa ta cigaban makarantar,” ya tabbatar.

Ya ce da ya zo wannan walima ta sauka ya yi magana da shugaban makarantar da aka yi saukar a kan bai ga kowa daga cikin wakilai na mazaɓar Rangaza ba, duk da kuwa akwai zaɓaɓɓen Kansila da mai gafaka a yankin.

Ya ja hankalinsu a kan duk irin wannan taro su riƙa sanya ‘yan siyasa a ciki, shi ne idan sun zo sun ga wata buƙata za a shiga domin a taimaka.

Hon. Sulaiman Isah Majidadin Zannan Kazaure, wanda kuma shi ne mai bai wa shugaban ƙaramar Hukumar Ungogo shawara a kan noma da kiwo ya ce, babu abin da za su ce da makarantar sai Allah ya saka wa masu gudanar da ita da alheri, “Domin duk makarantar da za ta kula da tarbiyyar yara da karatunsu da tsaftarsu, abu ne na ajinjina musu. Yara ne za a kawo musu ‘yan ƙasa da shekaru 10, amma su ba su kulawa har in ka kalli ɗanka za ka ga ya canza daga yanayin da ka kawo shi daga gida, abin yabawa ne da jin daɗi,” ya bayyana.

  • Related Posts

    Mataimakin Gwamnan Kano Ya Halarci Taron Maulidin Manzo (S) da Hon. Muktar Ishaq Ya Saba Shiryawa A Yakasai

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Murtala Sule Garo, ya yi kira ga al’ummar Musulmi, musamman matasa, da su yi koyi da rayuwa da koyarwar Annabi Muhammad…

    Iyayen Yara Sun Yaba Wa Makarantar Al-Burhan International College Bisa Yaye Mahaddata Al-Qur’ani Karo Na Huɗu

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Makarantar Al-Burhan International College da ke Bayan Wailaki a Jihar Kano, ta gudanar da bikin yaye mahaddata Al-Qur’ani karo na hudu. Da yake bayani kan kafuwar…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum