Abban Gandu Ya Tallafa Wa Masu Ƙananan Sana’o’i 400 Da Jari

Daga Ibrahim Muhammad

An bayyana cewa MD Alhaji Abba Aliyu Abubakar da aka sani da Abban Gandu da cewa tun sama da shekaru 10 yake yin hidimar ƙoƙarin tallafa wa mutane na ƙasa a cikin al’umma, musamman masu yin ƙananan sana’o’i, kama daga masu sayar da dankali, awara, ƙosai, waina, goro da sauran sana’o’i da jari don haɓɓaka harkokin da suke yi, kuma har yanzu yana cigaba da yi.

Alhaji Da’u Aliyu Abubakar Mai Unguwar Darmanawa, Kogunan Ƙasar Hausa, shugaban Abban Gandu Youths Mobilisation, wanda ya jagoranci rabon a madadin MD Abban Gandu ne ya bayyana hakan a wajen taron da aka yi na rabon tallafin jari ga mutane 400 a ƙaramar hukumar Birnin Kano.

Ya ce a baya sun raba tallafi ga mutum 500 a iya mazaɓar Gandun Albasa kaɗai, yanzu kuma MD Abban Gandu ya ce a faɗaɗa bayar da tallafin a dukkan mazaɓu 13 na ƙaramar hukumar Birnin Kano aka zaɓi mutum 100 masu ƙananan sana’o’i daga kowace mazaɓa aka ba su tallafin jarin.

Ya ce yanzu a sun kira mutane 400 ne aka ba su wannan jarin nan gaba kaɗan za a bai wa wasu ƙarin ragowar mutume 400 da zai zama adadin mutum 800 sun amfana ke nan, kuma suna da fatan nan gaba da yardar Allah suna da nufin faɗaɗa tallafin ga dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.

Ya shawarci mutane da suka amfana da wannan tallafin jarin da MD Abban Gandu ya ba su na ₦10,000 ga duk mai sana’a, su yi amfani da shi ta hanyar yin ƙoƙarin ƙara jarin sana’o’i da suke, domin nan da ‘yan watanni su bunƙasa sana’arsu su koyawa wasu.

Alhaji Da’u Aliyu Abubakar ya yi kira ga sauran mutane, musamman masu hannu da shuni su yi koyi da irin wannan tallafi da MD Abban Gandu yake bayarwa, la’akari da a yanzu ₦10,000 za ta taimaki mutum da shi da iyalinsa a kan ƙaramar sana’a. “Idan da za a sami masu irin wannan tallafin a duk ƙananan hukumomi za a samu rage raɗaɗin ƙuncin rayuwa,” ya tabbatar.

  • Related Posts

    Baffa Babba Ɗan’agundi Ya Ɗauki Nauyin Horas Da Matasa 156 Sana’o’in Dogaro Da Kai

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Babban Daraktan Cibiyar Kula da Nagartar Ayyuka ta Kasa (NPC), Hon. Dr. Baffa Babba Dan’agundi, ya dauki nauyin tarbiyantar da matasa 156 tare da koya musu…

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Baffa Babba Ɗan’agundi Ya Ɗauki Nauyin Horas Da Matasa 156 Sana’o’in Dogaro Da Kai

    Baffa Babba Ɗan’agundi Ya Ɗauki Nauyin Horas Da Matasa 156 Sana’o’in Dogaro Da Kai

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano