Daga Ibrahim Muhammad
Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta kai wa Mataimakin Sufetan ‘yan sanda Nijeriya mai kula da shiyya ta ɗaya ziyara a ofishinsa.
Ziyarar dai ta ƙunshi shugaban Hukumar, Shaikh Abba Abubakar Daneji, tare da sauran manyan Kwamishinonin Hukumar.
A ziyarar tasu sun tattauna muhimman batutuwa da za su taimaka wajen daƙile matsalar tsaro da tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano.
Hukumar Shari’a tana da gudunmawar da za ta bayar wajen taimaka wa jami’an tsaro, musamman wajen koyarwar da addinin Musulunci ya tanada domin ƙarfafa zaman lafiya
A nasa ɓangaren, mataimakin Sufetan ‘yan sanda mai kula da shiyya ta ɗaya AIG Ahmed Garba, ya bayyana jin daɗinsa bisa ziyarar, tare da tabbatar musu da samun cikakken goyon bayan rundunar ta dhiyya ta ɗaya a kowane lokaci.
Kakakin rundunar, CSP Bashir Muhammad ya ce, AIG Ahmed Garba zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran ɓangarorin tsaro na Kano da Jigawa wajen ganin an kare rayuka da dukiyoyin al’umma baki ɗaya.







