Daga Ibrahim Muhammad
Gidauniyar tallafa wa tagwaye maza da mata ta jihar Kano da ake kira Twins Brothers and Sisters Empowerment Foundation Kano,
ta gudanar da taron tallafawa mambobinta da karrama mutanen da suke tallafawa cigabansu.
Taron an gudanar da shi ne a rufaffen ɗakin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata ranar Asabar, ya sami halartar ɗimbin tagwaye maza da mata daga ciki da wajen jihar Kano.
Shugabanin ƙungiyar Alhassan Abdullahi da aka fi sani da Tukuntawa da Al-Hussain Abdullahi sun bayyana cewa taron dama duk shekara ana yin sa saboda ƙara haɗa kan tagwaye ne a duk inda suke a duniya ba a Kano ko ƙasar nan kaɗai ba.
Shi ya sa ma a wannan taron tagwayen sun zo ne daga jihohin Kebbi, Kaduna, Gwambe da sauran jihohi, kuma suna yi ne domin tagwaye da ba sa cikin tafiyarsu ga yadda Gidauniyar take taron su ma sun shiga a riƙa yi da su.
Sun ce tun da aka kafa gidauniyar a shekarar 2007 suke shirya irin wannan taron, kuma sun sami nasarori da yawa ciki har da daƙile ɗabi’ar nan ta yawon bara da ake yi da ‘yan biyu jarirai. Sun ɗauki mataki suna tallafa wa iyayen da suke irin wannan yawon baran da jariri idan sun ga buƙata ce ta sa suke barar.
Sun ƙara da cewa suna kuma haɗa auratayya a tsakaninsu, duk abin da ya shafi harkar bukin aure da suna da rashin lafiya idan ya taso suna shiga a tallafa wa tagwayen ƙarƙashin gidauniyar duk wannan hidima da kuɗin aljihunsu suke.
Yanzu daga irin ƙalubale da suke fuskanta akwai na ƙarancin kuɗaɗe na gudanarwa saboda yawa na suke da shi, don haka suna kira ga masu hali da shugabanni da ƙungiyoyi da ‘yan siyasa su shigo su riƙa tallafawa saboda abu ne da ake na taimakon al’umma domin har asibitoci suna zuwa bayar da gudunmuwar jini.
Alhassan Abdullahi da Alhusain Abdullahi tagwayen shugabannin Gidauniyar tallafa wa tagwaye maza da mata na jihar Kano sun ce taron na wannnan shekara sun yi ne tare da raba tallafin kayan abinci da jari ga marayu da iyayen tagwayen da karrama wasu muhimman mutane da suke ba da gudunmawa ga cigaban Gidauniyar.







