Ƙungiyar Tinubu/Zaura Ta Tallafa Wa mutane 300 Da Jarin Dogaro Da Kai A Dala, Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Ƙungiyar Tinubu/Zaura Organisation, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Jami’ar Siyasa Gangariya ta jihar Kano, Hon. Ado Garba Tati Dala, ta raba tallafin jarin dogaro da kai ga mutane 300 a ƙaramar hukumar Dala.

An gudanar da taron rabon tallafin ne a yammacin ranar Asabar a ɗakin taro na Mumbayya, inda Hon. Ado Garba Tati ya jaddada cikakken goyon bayan ƙungiyar ga tafiyar siyasar Hon. Abdussalam Abdulkarim (A.A.) Zaura, wanda ke neman tsayawa takarar Gwamnan jihar Kano a zaɓen shekarar 2027.

Da yake jawabi a wajen taron, Hon. Ado Garba Tati ya bayyana cewa jihar Kano ce cibiyar siyasa a Nijeriya, kuma a cikin Kano kuwa, ƙaramar hukumar Dala ce ke kan gaba wajen harkokin siyasa.

Ya ce taron da aka gudanar a Dala ya nuna irin gagarumin goyon bayan da al’ummar yankin ke bai wa A.A. Zaura, yana mai cewa babu wata ƙaramar hukuma a jihar da ta nuna irin wannan goyon baya a fili kamar Dala.

Ya ƙara da cewa dalilin da ya sa jama’a ke marawa A.A. Zaura baya shi ne halayensa na karamci, dattako, mutunci, haƙuri da kuma kulawa da al’umma da ’yan jam’iyya, duk kuwa da cewa ba shi da wani mukami a halin yanzu a gwamnati.

Hon. Tati ya ce a fahimtarsu, siyasa amana ce, adalci ce, kuma ibada ce, domin duk wani aiki na taimako, tausayi da gaskiya koyarwa ce ta addini.

A cewarsa, marawa mutum irin A.A. Zaura baya koyi ne da koyarwar addini.

Ya kuma tunatar da cewa wurin da aka gudanar da taron, gidan marigayi Malam Aminu Kano, wuri ne da aka gina tubalin siyasar manufa da aƙida, inda suka taso suna koyon siyasa, tare da manyan jagorori irin su marigayi Lili Gabari, Dambazau, Aminu Inuwa da Asabe Raza.

Shugaban ya ce su a ƙaramar hukumar Dala suna tafiyar da siyasa ta tsafta da amana, suna kuma girmama dukkan masu neman takara a jihar Kano.

Ya ƙara da cewa su mambobin jam’iyyar APC ne masu biyayya, kuma duk ɗan takarar da jam’iyya ta tsayar suna shirye su mara masa baya, sai dai zaɓinsu a wannan lokaci shi ne A.A. Zaura saboda cancanta da ingancinsa.

A cewarsa, A.A. Zaura mutum ne ɗan kasuwa daga cikin manyan ’yan kasuwa a duniya, wanda ke taimaka wa jama’a da kuɗin aljihunsa, ba tare da dogaro da dukiyar gwamnati ba.

Hon. Ado Garba Tati ya jaddada cewa goyon bayan da suke bai wa A.A. Zaura ya samo asali ne daga irin hidimar da yake yi wa al’umma da halaccin dukiyarsa, yana mai cewa hakan ne ya sa suke masa biyayya tare da mara masa baya a takarar Gwamna.

Taron ya samu halartar ɗaya daga cikin daraktocin gidan siyasar A.A. Zaura, kuma tsohon ɗan majalisar tarayya daga Nasarawa, Sani Baban Kowa, wanda ya yaba wa Hon. Tati bisa shirya taron da kuma rabon tallafin jarin dogaro da kai.

Ya ce wannan aiki abin koyi ne da ya dace da ßabi’un A.A. Zaura na taimakon al’umma.

Dubban ’yan jam’iyyar APC, maza da mata, tare da shugabannin siyasa da tsofaffin masu riƙe da muƙamai a ƙaramar hukumar Dala ne suka halarci taron.

A yayin taron, an miƙa kyautar karramawa ga A.A. Zaura, inda Sani Baban Kowa ya karɓa a madadinsa.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum