Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Sabon Wamban Gwagwarwa a ƙaramar hukumar Nassarawa a jihar Kano, Alhaji Isma’ila Abdullahi Haske, ya bayyana cewa naɗin sarautar da aka yi masa wata babbar ƙarfafawa ce gare shi domin ƙara himma da jajircewa wajen hidimtawa al’ummar Gwagwarwa.
Alhaji Isma’ila Haske ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da ’yan jarida jim kaɗan da kammala bikin naɗin, inda ya nuna godiyarsa ga Allah Maɗaukakin Sarki da Ya nuna musu wannan rana ta farin ciki da suka daɗe suna jira tsawon kusan shekaru biyu kafin a tabbatar da sarautar.
Ya kuma miƙa godiya ta musamman ga Dagacin Gwagwarwa, Alhaji Usman Sanusi Aliyu, bisa yadda ya ba su dama da amana domin su ci gaba da hidimtawa al’umma ta hanyar ɗora musu wannan muƙami na gargajiya.
Sabon Wamban ya ce sarautar da aka ba su ba tasu kaɗai ba ce, illa ta al’umma baki ɗaya, domin cancanta aka bi wajen bayar da ita, sakamakon irin gudunmawa da hidimomin da suke bayarwa ga jama’a.
Ya ce ba su da wata magana face godiya ga Allah da kuma dukkan al’ummar Gwagwarwa da suka bayar da gudunmawa wajen tabbatuwar wannan al’amari.
Alhaji Isma’ila Haske ya ƙara jaddada godiyarsa ga Dagacin Gwagwarwa bisa goyon baya da jagoranci da ya bayar wajen tabbatar da naɗin, yana mai bayyana Gwagwarwa a matsayin gari mai tarihin gwagwarmaya, inda kakanni suka yi ƙoƙari sosai wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a cikinsa.
Ya ce babban aikin Wambai a masarautar Gwagwarwa shi ne kula da al’umma da haɗa kan jama’a, musamman ganin yadda Allah Ya albarkaci garin da kasancewar kabilu da harsuna daban-daban daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
A cewarsa, wannan ne ya sa suka ɗauki naɗin a matsayin nauyi da amanar da za su ci gaba da aiwatarwa domin bunƙasa cigaba da walwalar al’ummar Gwagwarwa.







