Manoma Sun Nemi Gwamnati Ta Tallafa Musu Kan Asarar Hatsi

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Shugaban Ƙungiyar Masu Sayar da Masara ta Kasuwar Dawanau, Alhaji Jamilu Abdullahi, ya yi kira ga gwamnatoci a matakai daban-daban da su ɗauki matakin gaggawa domin kawo daidaito a harkar kasuwancin kayan amfanin gona, tare da tallafa wa manoma da suka tafka asara sakamakon faduwar farashin hatsi.

Alhaji Jamilu, wanda kuma shi ne shugaban Ƙungiyar Manoma da Masu Sayar da Kayan Amfanin Gona ta Ƙasa a Jihar Kano (Amana Farmers and Grains Suppliers Association), ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Kano.

Ya ce sauyin farashin kayayyaki a kasuwa wani abu ne da aka saba da shi yau da kullum, domin Allah ne ke jujjuya lamuran rayuwa; wani lokaci farashi yana ƙaruwa, wani lokaci kuma yana raguwa.

Sai dai ya jaddada cewa sauƙin da aka samu a farashin hatsi a halin yanzu ya jefa manoma da dama cikin mawuyacin hali.

A cewarsa, yawancin manoma ba sa kuka ne kan ganin kayan abinci sun yi araha, illa damuwarsu ita ce rashin daidaito. Ya ce manomin ƙauye na da buƙatun rayuwa da dama da yake dogaro da noman da ya yi wajen biya, kamar shirye-shiryen aure, aurarwa ko wasu muhimman lamurra na rayuwa.

“Idan amfanin da manomi ya noma ya karye raga-raga, to idan yana da wata buƙata, dole ya sayar da amfanin gonarsa da araha, amma idan ya je kasuwa sai ya sayi kayan da yake buƙata a tsada,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa daidaito tsakanin farashin sayarwa da na sayayya shi ne abin da ya fi amfani ga manoma.

Alhaji Jamilu ya bayyana cewa ‘yan kasuwa kan sayar da kaya gwargwadon yadda suka saya, amma halin da manomi ke ciki ya fi buƙatar tausayi, duba da irin wahalar da ya sha a noma, da kuma kuɗin da ya kashe wajen sayen takin zamani da sauran kayayyakin noma, alhali amfanin da ya samu ya yi sauƙin farashi.

Ya yi nuni da cewa ko manomin da ya noma buhunan hatsi da yawa, idan farashi ya karye, ba lallai ne hakan ya wadatar da shi wajen biyan manyan buƙatun rayuwarsa ba.

Ya ce galibin manoma ba su da wata sana’a face noma, don haka duk wani sauyi da ya shafi amfanin gonarsu na shafar rayuwarsu kai tsaye.

Shugaban ƙungiyar ya ce a baya jama’a suna kuka kan tsadar kayan abinci, wanda hakan ya sa gwamnati ta mayar da hankali wajen ganin farashi ya sauka. Sai dai yanzu da aka samu yalwar noma kuma farashi ya karye, manoma ne ke cikin wahala.

Ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ba ta ɗauki matakin da ya dace ba, nan gaba noman na iya raguwa, sakamakon sarewar gwiwar manoma.

Don haka ya buƙaci gwamnati da ta nemo hanyoyin da za su kawo daidaito a kasuwar kayan amfanin gona, tare da ɗaukar matakan da za su rage raɗaɗin da manoma ke ciki.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum