Kano: ’Yan Sanda Sun Kama Mutane 3 Kan Kisan Wata Mata da ’Ya’yanta 6

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cafke mutane uku da ake zargi da hannu a kisan gillar wata mata da ’ya’yanta shida, wanda ya faru a unguwar Ɗorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Lahadi.

A cewar sanarwar, kamen ya biyo bayan wani aiki na musamman da rundunar ta gudanar bisa sahihan bayanan sirri, ƙarƙashin umarnin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, tare da kulawa ta musamman daga Kwamishinan ’Yan Sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori.
Rundunar ta bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne a wani samame da aka gudanar daga ƙarfe 10:00 na dare a ranar 17 ga Janairu zuwa ƙarfe 4:00 na asubahin ranar 18 ga Janairu, 2026.

Waɗanda aka cafke sun haɗa da Umar Auwalu, mai shekaru 23 daga unguwar Sabuwar Gandu; Isyaku Yakubu da aka fi sani da “Chebe”, mai shekaru 40 daga unguwar Sagagi; da Yakubu Abdulaziz, wanda aka fi kira “Wawo”, mai shekaru 21 daga unguwar Sabon Gida Sharaɗa.

Rundunar ta ƙara da cewa wanda ake zargi da jagorantar kisan, Umar Auwalu ɗan’uwar marigayiyar ne, ya amsa aikata laifin.

Haka kuma, ya bayyana wa masu bincike cewa sun aikata wasu kashe-kashe masu tayar da hankali a wasu sassan jihar Kano a kwanakin baya.

Daga cikin kayayyakin da ’yan sanda suka ƙwato daga hannun waɗanda ake zargin akwai tufafi masu tabon jini, wayoyin salula guda biyu na marigayiyar, adda, gora, kuɗaɗe da ake zargin an kwace daga wurin da lamarin ya faru, da kuma wasu makamai masu haɗari. Rundunar ta ce bincike na ci gaba domin gano cikakken bayanin lamarin da kuma yiwuwar kama wasu da ke da hannu a ciki.

A ƙarshe, rundunar ’yan sandan jihar Kano ta yaba wa jami’anta bisa ƙwazon da suka nuna wajen gudanar da aikin, tare da gode wa al’ummar jihar bisa addu’o’i, goyon baya da haɗin kai da suke bai wa jami’an tsaro.

Rundunar ta kuma tabbatar wa jama’a aniyar ta na ganin an gurfanar da duk masu aikata laifuka a gaban kuliya domin su fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum