Rasuwar Alhaji Bature Abdul’aziz Babban Rashi Ne Ga ’Yan Kasuwa A Kano Da Ƙasa Baki Ɗaya -Ibrahim Ɗanyaro

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Shugaban Dattawan Kasuwar Muhammad Abubakar Rimi da Singa na jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ɗanyaro, ya bayyana rasuwar fitaccen ɗan kasuwa Alhaji Bature Abdulaziz a matsayin babban rashi ga ’yan kasuwa a jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Alhaji Ibrahim Ɗanyaro ya bayyana hakan ne yayin da yake nuna alhini da jimamin rasuwar marigayin, wanda ya ce ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen haɓaka harkokin kasuwanci da kuma ci gaban tattalin arziƙi a Kano da Nijeriya baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa marigayi Alhaji Bature Abdulaziz, mutum ne mai son shiga duk wata harka da ta shafi jin ƙai da walwalar al’umma, musamman waɗanda za su taimaka wa talakawa.

A cewarsa, marigayin shi ne shugaban Abokan Asibitin Murtala, wata ƙungiya mai zaman kanta wadda ke tallafa wa marasa lafiya, bayan rasuwar marigayi Baban Ladi.

A ƙarshe, Alhaji Ibrahim Ɗanyaro ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki ya ji ƙan marigayi Alhaji Bature Abdulaziz, ya gafarta masa, ya sanya Aljanna Firdausi ta zama makomarsa, tare da bai wa iyalansa da ’yan’uwansa haƙurin jure wannan babban rashi.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo