Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Shugaban Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi reshen Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Muhammad, ya roƙi Gwamnatin Jihar Kano da ta daidaita bambancin albashi tsakanin ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi.
Kwamared Ibrahim ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a bikin Ranar Ma’aikata ta Duniya, inda ya ce ranar ma’aikata rana ce mai muhimmanci da farin ciki ga ma’aikata a fadin duniya.
Ya ce halin tsadar rayuwa da ake ciki a ƙasar nan abin damuwa ne ga kowa, ba ma’aikata kaɗai ba. “Idan komai ya yi sauƙi, kowa zai samu sauƙi,” in ji shi.
Duk da haka, ya nuna godiya ga Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa ƙarin albashin da aka yi wa ma’aikata, wanda ya ce abin farin ciki ne a gare su.
A cewarsa, tun bayan hawan gwamnatin Abba, an samu kyakkyawar dangantaka tsakanin gwamnati da ma’aikatan ƙananan hukumomi, inda ya ce ma’aikata na karɓar albashinsu a kan lokaci.
Haka kuma, ya ce gwamnati na biyan haƙƙoƙin ma’aikatan da suka yi ritaya, ciki har da kuɗaɗen fansho da garatuti.
Ya ƙara da cewa zuwa yanzu gwamnati ta biya sama da Naira biliyan 32 daga cikin Naira biliyan 48 na garatutin da ta gada, yana mai cewa ana sa ran kafin ƙarshen wa’adin mulkinsa na farko, za a kammala biyan sauran bashin.
Sai dai ya buƙaci gwamnati da ta cike gibin albashi da ke tsakanin ma’aikatan jiha da na ƙananan hukumomi. “Makaranta ɗaya muka je, wuri ɗaya muke aiki, kuma aiki ɗaya muke yi. Don haka muna fata a daidaita mana albashi yadda ba za a sami bambanci ba,” in ji shi.
Haka zalika, ya yi kira ga ma’aikatan ƙananan hukumomi da su ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Dangane da batun cin gashin kan ƙananan hukumomi, Kwamared Ibrahim ya ce suna fatan a aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli ta Nijeriya da ta tabbatar da cin gashin kai ga ƙananan hukumomi, yana mai cewa har yanzu ba a fara aiwatar da hukuncin ba.
Ya kuma yabawa tsarin da Gwamnatin Kano ke bi na bai wa kowace ƙaramar hukuma damar aiwatar da ayyukan da ta gabatar bayan tantancewa, amma ya ce sun fi son a riƙa tura kuɗaɗen ƙananan hukumomi kai tsaye domin samun ingantaccen ci gaba.
“Ƙananan hukumomi su ne tushen ci gaban ƙasa. Idan aka ba su ‘yancin cin gashin kai, za a samu ci gaba sosai,” in ji shi.







