Daga Dokajin Kano Zuwa Sarkin Sudan: Abin Farin Ciki Ne -Injiniya Aminu Aliyu Wudil

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Injiniya Aminu Aliyu Wudil, Wamban Sarkin Sudan na Kano, ya bayyana farin cikinsa bisa naɗin Alhaji Muhammad Aliyu Wudil a matsayin Sarkin Sudan na Kano, wanda Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi II ya yi masa a ranar Juma’a a fadarsa.

Ya ce ɗaukakar da aka yi wa Alhaji Muhammad Aliyu Wudil daga sarautar Dokajin Kano zuwa Sarkin Sudan babban abin alfahari ne ga iyalai da al’ummar yankin baki ɗaya.

A cewarsa, yawan jama’ar da suka halarci bikin naɗin domin taya murna daga sassa daban-daban na nuna irin kyakkyawar mu’amala, halin kirki da kuma taimakon jama’a da sabon Sarkin Sudan ke da shi, wanda ya jawo masa karɓuwa a zukatan mutane.

Injiniya Aminu Aliyu Wudil ya ƙara da cewa, kamar yadda aka naɗa sabon Sarkin Sudan a shekarar 2023 a matsayin Dallatun Kano daga bisani ya zama Dokaji, yanzu kuma ya samu ƙarin ɗaukaka zuwa Sarkin Sudan, yana mai fatan Allah ya ba shi ikon gudanar da wannan sabon matsayi cikin nasara da kwanciyar hankali.

Haka kuma, ya yi addu’ar Allah ya saka wa Sarkin Kano da alkhairi, ya ƙara masa lafiya da tsawon rai, tare da fatan alheri ga sabon Sarkin Sudan a sabuwar rawar da zai taka.

  • Related Posts

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2027 mai kimanin Naira Tiriliyan 1.107 ga Majalisar Dokokin jihar Kano, inda ya…

    Takarar Majalisar Jaha Da Nake A ADP Amsa Kiran Al’ummar Gwale Ne -Dakta Bashir Aliyu Galadanci

    Dag Ibrahim Muhammad Kano Dan takarar majalisar dokokin Jihar Kano a Karamar Hukumar Gwale a jam’iyyar ADP, Dakta Bashir Aliyu Galadanci, ya bayyana cewa al’ummar karamar hukumar ne suka matsa…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum