Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Masu ruwa da tsaki na mazabar Kiru da Bebeji, Kano, sun amince baki ɗaya da tsayar da Abdulmumin Jibril Kofa domin sake neman kujerar Majalisar Wakilai karo na biyar a jere.
An cimma wannan matsaya ne bayan gudanar da shawarwari masu zurfi da kuma fahimtar juna tsakanin manyan shugabannin siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a faɗin mazaɓar.
Shugaban taron masu ruwa da tsakin, Ahmad Ali Yako, ne ya bayyana hakan, inda ya ce an yanke shawarar ne bisa la’akari da kyakkyawan tarihin wakilcin Kofa da kuma ƙoƙarinsa na bunƙasa yankunan karkara.
Ya ƙara da cewa mazaɓar ta samu ci gaba da haɗin kai a ƙarƙashin wakilcin Kofa, yana mai jaddada cewa ci gaba da ba shi dama zai taimaka wajen ƙarfafa nasarorin da aka riga aka samu.
A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa masu ruwa da tsakin bisa cimma matsaya guda.
Ya bayyana hakan a matsayin alamar balagar siyasa da haɗin kai, tare da gode musu kan fifita muradin al’umma sama da buƙatun kai.
Gwamnan ya kuma buƙace su da su ci gaba da riƙe wannan haɗin kai yayin da ake tunkarar zaɓukan da ke tafe.
Ana kallon wannan matsaya a matsayin wani gagarumin ƙarin ƙarfi ga matsayin siyasar Kofa yayin da ake shirin zagayowar zaɓe mai zuwa.






