Daga Ibrahim Muhammad, Kano
(Ɗaukar nauyin wallafawa: Hon. Muhammad Adamu Bomboy)
Al’ummar Ƙaramar Hukumar Nasarawa ta Jihar Kano sun bayyana gamsuwarsu da irin wakilcin da Hon. Hassan Shehu Husain ke yi a Majalisar Wakilai ta Tarayya, sakamakon ayyukan ci gaba da ya kawo yankin tun bayan hawansa majalisa.

Masu magana da yawun al’ummar yankin sun ce irin namijin ƙoƙarin da ɗan majalisar yake yi ne ya sa suka amince da ci gaba da mara masa baya, musamman a wannan lokaci da siyasar jihar Kano ke ɗaukar sabon salo.

Sun bayyana cewa kafin zuwan Hon. Hassan Shehu Husain, wanda ya gaji kujerar daga hannun ɗan majalisar da ya shafe wa’adi uku yana wakiltar mazaɓar, ba a samu irin waɗannan ayyukan ci gaba da suka amfani al’ummar Ƙaramar Hukumar Nasarawa ba.

Fitaccen ɗan siyasa kuma mai goyon bayan tafiyar Hon. Hassan Shehu Husain, Hon. Muhammad Adamu Bomboy, ya bayyana cewa tura shi majalisa babbar nasara ce ga al’ummar yankin.
A cewarsa, babban aikin ɗan majalisa shi ne gabatar da ƙudurori da samar da dokoki masu amfani ga al’umma, inda ya ce tun bayan zuwan Hon. Hassan majalisa ya gabatar da muhimman ƙudurori masu yawa da suka shafi ci gaban Karamar Hukumar Nasarawa, Jihar Kano da ƙasa baki ɗaya.

Ayyukan Ci Gaba
Hon. Bomboy ya lissafo wasu daga cikin ayyukan da aka gudanar a yankin ƙarƙashin wakilcin Hon. Hassan Shehu Husain.
Ya ce an gina tituna a wasu unguwanni da sama da shekaru 57 zuwa 70 ba a taɓa tsammanin za a kai musu kwalta ba.
A ɓangaren samar da ruwa, ya ce an samar da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana a dukkan mazaɓu 11 na ƙaramar hukumar.
Haka kuma, domin inganta tsaro, an sanya fitilun masu amfani da hasken rana a mazaɓu daban-daban na yankin.
A ɓangaren ilimi kuwa, ya ce an ɗauki nauyin karatun matasa maza da mata, tare da gina ajujuwa a yankunan Hotoron Arewa, Dakata da Tudun Wada.

Ya ƙara da cewa an gina tsangayu tare da gyaran wasu makarantu, sannan an samar da kujeru da kayan koyarwa domin inganta harkar ilimi.
A ɓangaren lafiya kuwa, Hon. Bomboy ya ce an gina cibiyar kula da lafiya ta matakin farko a Mazaɓar Hotoron Arewa, wadda aka kammala tare da miƙa ta ga ƙaramar hukuma domin ɗaukar ma’aikata da fara aiki.
A cewarsa, asibitin zai taimaka matuƙa wajen kula da lafiyar al’ummar yankin da ma maƙwabtan mazaɓun da ke kusa.
Ya kuma yaba da irin manufofin Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, musamman a ɓangarorin ilimi, lafiya da ci gaban matasa, yana mai cewa Hon. Hassan na koyi da irin salon shugabancinsa.
Hon. Bomboy ya ƙara da cewa tun bayan shekarar 1999 ba a taɓa samun ɗan majalisar tarayya daga yankin Nasarawa da ya bayar da tallafi ga al’umma da matasa kamar Hon. Hassan Shehu Husain ba.
Ya ce mutane da dama sun amfana da tallafi iri-iri, inda wasu suka samu babura da motoci, yayin da aka tallafa wa mata da jari, injinan niƙa da kekunan ɗinki domin dogaro da kai.
Kira Ga Al’umma

Hon. Bomboy ya yi kira ga al’ummar Kano da masu ruwa da tsaki a Ƙaramar Hukumar Nasarawa da su ci gaba da bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf da Hon. Hassan Shehu Husain goyon baya domin tabbatar da ɗorewar ayyukan ci gaba a zaɓen 2027.
Ya ce Ƙaramar Hukumar Nasarawa tamkar ƙaramar Nijeriya ce saboda yadda ƙabilu daban-daban ke rayuwa a cikinta cikin zaman lafiya da haɗin kai.
Haka kuma, ya buƙaci al’umma da su ci gaba da kai buƙatunsu da matsalolinsu ga shugabanni domin nemo hanyoyin magance su.
Ya yaba da yadda ƙofar ofishin Hon. Hassan ke buɗe ga kowa da kowa, yana mai cewa duk wata buƙata da za ta amfani al’umma ana sauraron ta tare da ɗaukar matakan da suka dace.
“A duk ƙarshen mako yana dawowa daga Abuja domin sauraron buƙatun jama’a a ofishinsa daga ranar Juma’a zuwa Lahadi,” in ji shi.

A ƙarshe, Hon. Bomboy ya bayyana cewa ayyukan da Hon. Hassan Shehu Husain ke gudanarwa sun samu yabo daga Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda har ya buƙaci sauran ‘yan majalisa da su yi koyi da shi.
Ya bayyana fatan cewa al’ummar mazaɓar za su sake ba shi dama a zaɓen 2027 domin ci gaba da ayyukan raya ƙasa da ci gaban al’umma.






