Daga Ibrahim Muhammad Kano.
An bayyana ɗan majalisar jihar Kano mai wakiltar Gezawa, Hon. Abdullahi Yahaya Tsamiyar Kara, Barden Gezawa, a matsayin mutum mai ƙoƙarin sauke nauyin jagorancin al’ummar ƙaramar hukumar.
Hon. Sani Muhammad Jogana, jigo a jam’iyyar APC a Gezawa kuma ɗaya daga cikin hadiman ɗan majalisar, ne ya bayyana haka game da nasara da ɗan majalisar ya samu na sake sahale masa yin takara na majalisar dokokin jihar Kano na Gezawa a zabe mai zuwa.
Ya ce tun zuwan Hon. Abdullahi Yahaya Tsamiyar Kara majalisar dokokin jihar Kano, a lokacin da suke marasa rinjaye, ya yi ƙoƙari wajen kai kudire-kudire da kawo ayyuka daban-daban da al’umma ke bukata a yankin.
Ya ƙara da cewa ɗan majalisar na Gezawa yana iya ƙoƙarinsa wajen tallafawa matasa, mata, ‘yan siyasa da sauran al’umma. Idan yana gida, za ka ga dubban mutane a ƙofar gidansa saboda yadda yake rungumar kowa.






