Tsayar da Nasir Ja’oji Takarar Majalisar Tarayya A Tarauni Da APC Ta Yi, Babbar Dama Ce Ga Cigaban Al’ummar Yankin — Balaraba Ibrahim KAPAG

Daga Ibrahim Muhammad Kano

An bayyana cewa Hon. Nasir Bala Ja’oji, wanda ya sami nasarar zama ɗan takarar majalisar tarayya na ƙaramar hukumar Tarauni a jam’iyyar APC, tun kafin ya sami wata dama ta muƙami matashi ne da yake taimakawa al’umma.

Hajiya Balaraba Ibrahim, tsohuwar mai baiwa tsohon Gwamnan Kano shawara kan ma’adanai kuma shugabar ƙungiyar KAPAG, ce ta bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai.

Ta ce tun kafin ya sami wani muƙami na gwamnati, yana gina rijiyoyin burtsatse, tallafawa mabukata da marasa lafiya a asibiti, raba kayan abinci a lokacin azumi, da sauran hidimomi da yawa da yake yiwa maza da mata.

Ta ƙara da cewa Hon. Nasir Ja’oji matashi ne mai arziki, mai taimako, mai son ci gaban al’umma. Ya shiga siyasa ba don neman kuɗi ba, sai don samun damar yin fiye da abin da yake yi a baya na tallafawa ci gaban al’umma.

Hajiya Balaraba ta ce samun nasarar tsayar da Ja’oji a matsayin ɗan takarar majalisar tarayya na ƙaramar hukumar Tarauni a APC dama ce a gare shi ta shiga siyasa domin cigaba da tallafawa al’ummar Tarauni da jihar Kano baki ɗaya.

Ta ce suna godiya ga Allah bisa yadda abubuwa na alkhairi ke faruwa, duk da cewa komai yana da kalubale a rayuwa.

Suna kuma godiya ga Gwamnan jihar Kano, Injiniya . Abba Kabir Yusuf, da tsohon Gwamnan jihar Kano kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, bisa kai kawo da suka yi na tabbatar da an yi sulhu tsakanin masu neman takara a jihar Kano.

Hajiya Balaraba Ibrahim ta taya Alhaji Murtala Sule Garo murna bisa zaɓarsa a matsayin mataimakin Gwamnan jihar Kano. Ta yi masa addu’ar samun nasara wajen haɗa kai da Gwamna domin ci gaban Kano.

Ta ce ƙungiyar KAPAG, wadda aka kafa tun 1999, ta saba wayar da kan matasa kan sanin kansu da tsare mutuncinsu. Yanzu ƙungiyar ta zauna a bayan jam’iyyar APC, tana bai wa ‘yan takarar da ta tsayar a kowane mataki goyon baya.

Ta kuma nuna jin daɗi da farin cikinta bisa nasarar Ubangidansu a siyasa, Sanata Barau I. Jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattawa ta ƙasa, bisa samun takarar Sanatan Kano ta Arewa ta hanyar sulhu da aka yi.

Hajiya Balaraba Ibrahim ta shawarci ‘yan takarar jam’iyyar APC da suka samu nasara kar su manta da alkawarin da suka yiwa waɗanda suka janye musu suka yarda aka yi sulhu aka bar musu takara. Ya kamata su jawo su a jiki, su yi mu’amala da su, idan akwai damar ba su aiki su ba su. Wannan zai ƙara haɗin kai da taimaka wa al’umma a jihar Kano.

Ta ƙare da cewa suna fatan Allah ya sa a yi zaɓen 2027 lafiya, jam’iyyarsu ta APC da dukkan ‘yan takararsu su sami nasara tun daga Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu, da gwamnoni, sanatoci, da ‘yan majalisun jiha da na tarayya.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum