Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Ɗaya daga cikin masu neman takarar gwamnan jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Ibrahim Little, ya bayyana rashin amincewarsa da zaɓen fid-da-gwani na Gwamna da ɓangaren magoya bayan Malam Ibrahim Khalil suka gudanar.
A wata sanarwa da Mataimaki na Musamman ga Ibrahim Little, Mukhtar Adnan, ya fitar, ya ce ɓangarensu bai shiga cikin zaɓen ba, saboda a cewarsa ba a gudanar da shi bisa umarnin uwar jam’iyyar ta ƙasa ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa ba a gudanar da zaɓen bisa ƙa’ida ba, inda ta yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankalinsu tare da jiran lokacin da uwar jam’iyyar ADC ta ƙasa za ta ayyana domin gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani na takarar Gwamnan jihar Kano.






