Zaɓar Jam’iyyar PDP A 2027 Zai Kawo Gyara Da Kyautata Rayuwar Al’ummar Jihar Kano Da Kasa Baki Ɗaya -Hajiya Khadija Ɗahiru Gama

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Jam’iyyar PDP ta na kara kaimi wajen tuntubar mata a lungu da sakon jihar Kano domin wayar da kan su kan halin da kasar ta shiga da kuma yadda jam’iyyar ta shirya domin tabbatar da samar da farin ciki da walwalar mata da matasa a fadin kasar baki daya idan ta.kafa Gwamnati.

Mataimakiyar Shugabar Mata ta jam’iyyar PDP ta Jihar Kano, Hajiya Khadija Dahiru Gama, ce ta bayyana hakan.Ta ce akwai abubuwa masu muhimmanci da mata da al’ummar kasar nan baki daya ya kamata su tuna da su a lokacin da PDP ke mulki.

“A lokacin mulkin PDP kasarnan na cikin kwanciyar hankali, walwala da saukin rayuwa.da samun ilimi mai inganci da kyautatuwar harkar lafiya. Amma a yanzu duk wadannan abubuwa sun gushe. Kowa yana cikin rudani a kowane bangare ” in ji ta.

Hajiya Khadija ta ce ba sai an gaya wa ‘yan Nijeriya jam’iyyar da za su zaba ba, domin PDP ita ce hanya kawai ta kawo gyara. Ta bayyana damuwarta kan yadda rashin tsaro ya karu, inda ake fadan daba da rana tsaka a Kano ana kisan kai ba wani mataki da ake dauka harkar ilimi ya tabarbare.

“Mu iyaye mata ba ma jin dadin ganin ‘ya’yanmu basa samun ilimi.Domin Ilimi shine tushen tarbiyya. Amma a yanzu aji daya za ka samu a cushe dalibai sama da 200, wanda a ka’idar koyarwa ba haka ba ne. Babu abin da yaro zai fahimta a irin wannan yanayi, kuma rayuwa ta zama ‘hannu baka, hannu kwarya’. Wannan yana matukar damun mata a Kano da Najeriya baki daya,” in ji ta.

Mataimakiyar shugabar Mata ta PDP ta ce a yanzu haka jam’iyyar tana wayar da kan mata da matasa da su dage su yi katin zabe, domin kuri’ar su ita ce ‘yancinsu da ita za su canza duk abin da suke so su canza.

Ta bayyana cewa saboda nisa, wasu na fama da wahalar rayuwa basa iya zuwa ofishin INEC suyi katin zaben don wasu a cikin jam’iyyar PDP suke daukar nauyin mutane, su ba su kudin mota su je su yi katin. Muna ganin hakan a matsayin hanya daya ta sama musu dama ta kubuta daga halin da ake ciki lokacin zabe da katin zabensu,” in ji ta.

Hajiya Khadija ta ce PDP tana da kwarin gwiwa kan dukkan ‘yan takararta na kowane mataki. Dan takarar Gwamnan Kano na PDP, Alhaji Muhammad Dalhatu, mutum ne nagari wanda ba shi da tambari mara kyau a siyasa ko a mu’amala.

“Ya san ciwon matasa. Ya na fadi tashi a cikin al’umma, kuma yana da gogewa wajen sanin halin da al’umma suke ciki. Shi ne zai fitar da Kano daga halin da take ciki da yardar Allah in ya zama Gwamna,” in ji ta.

Ta kara yin kira ga al’ummar Kano da Najeriya baki daya su fito su yi katin zabe domin canza “?wanna gwamnatin zalunci a kowane mataki”.

Ta ja hankalin jama’a da cewa: “Duk wanda ya ba ku kudi domin ku zabe shi, ku karba. Amma karbar kada tasa Ku zabi wanda ba zai kawo muku sauyi ba, domin hakkin ku ne aka baku, ba taimako ba ne.”

Hajiya Khadija Dahiru Gama ta kuma roki mambobin PDP da ‘yan takara da shugabanni su kara dagewa wajen fito da manufofin jam’iyyar da kuma tallata ta sosai ga al’umma.

  • Related Posts

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Sakamakon irin dimbin alheri da gudummawar da dan takarar majalisar tarayya na PDP, Hon. Alhaji Abubakar Ibrahim Maina, ke bai wa al’ummar karamar hukumar Tarauni, al’ummar…

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo