Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Dan siyasa jigo a jam’iyyar APC a jihar Kano dan Karamar Hukumar Ungogo, Alhaji Naziru Alasan Abdullahi, ya bayyana burin jam’iyyarsa na baiwa shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu da Gwamna jihar Kano.Abba Kabir Yusuf kuri’u miliyan 5 zuwa 6 daga jihar Kano domin.tabbatar da nasarar su a zaben 2027 mai zuwa.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen rabon tallafi ga mata 1,000 da Shugabar Matan Kungiyar City Boy ta Kasa, Hajiya Ummulsalama Isyaku Rabiu, ta gudanar a Kano.
Alhaji Naziru, wanda jigo ne a Kamfanin Takin Zamani na Boko, ya ce ƙuri’un da al’ummar Kano za su ba Tinubu da Abba alama ce ta gamsuwa da amincewa da yadda APC ke mulki a matakin kasa da na jihar.
“Wannan ƙuri’ar za ta kuma nuna wa ‘yan adawa cewa APC ce kan gaɓa wajen ƙarɓuwa a tsakanin al’ummar Kano saboda kyautatawa da take,” in ji shi.
Ya jaddada cewa ba wasa suka zo yi ba a siyasa. “Za mu yi aiki tuƙuru don tabbatar da nasaar APC a kowane mataki a jihar Kano da Najeriya baki ɗaya,” in ji Alhaji.Naziru.
Jigo a jam’iyyar na APC Alhaji Naziru Alasan Abdullahi ya shawarci al’ummar Kano da ba su da katin zabe su fito da gaggawa su yi rajista.don Katin zabe shi ne makamin da za ku yi amfani da shi wajen ba wa jam’iyyar APC kuri’a.”
Ya kara da cewa, “Abu ne na alfahari a ce Bola Tinubu ne Shugaban Kasa. Mutum ne nagari, duk inda ka je a duniya za a girmama ka da sunan kasar.”
Alhaji Naziru ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da ‘yan Najeriya da su sake zaben shugaban kasa Tinubu da gwamna jihar Kano.Abba da sauran ‘yan takarar APC a kowane mataki a 2027. Domin ci gaba da ganin ayyukan raya kasa da ke gudana.
A ƙarshe ya bayyana cewa rabon tallafin da Shugabar City Boy ta Mata ta Kasa, Hajiya Ummulsalama Isyaku Rabiu ta yi wa mata 1,000, somawa akayi nan gaba kadan za a sake gudanar da irin wannan tallafi ga sauran dinbin al’umma.






