Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta tallafa wa masu sana’ar saye da sayar da wayoyin hannu (GSM), musamman ‘yan kasuwa masu ƙaramin ƙarfi, domin bunƙasa sana’ar da kuma ci gaba da samar da ayyukan yi ga matasa.
Wannan kira ya fito ne daga Mai Binciken Kuɗi na Ƙungiyar Kasuwar GSM ta ‘Yan Kura, Malam Auwal Baffa Taura, yayin da yake zantawa da manema labarai a madadin shugabannin kasuwar.
Malam Auwal ya bayyana cewa, duk da cewa ƙungiyar tana da gidauniyar tallafa wa ‘yan kasuwa da shugabanninta suka kafa, wadda ke taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi su fara sana’a ko su bunƙasa ta, har yanzu suna buƙatar gwamnatin jihar ta ƙara ba su goyon baya.
“Idan ka duba, wani zai zo kasuwa ba shi da wurin zama. Amma da ikon Allah da tallafin da ake samu, sai a samar masa da wajen sana’a, ya fara kasuwanci, daga baya ma ya zama yana taimaka wa wasu,” in ji shi.
Ya ce a halin yanzu suna zaune lafiya da abokan hulɗarsu, suna mutunta shugabanci da hukumomin gwamnati, tare da addu’ar Allah Ya ci gaba da ba Najeriya zaman lafiya da tsaro.
Malam Auwal ya ce harkar saye da sayarwa da kuma gyaran wayoyin hannu ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan yi ga dubban matasa masu dogaro da kai a Jihar Kano.
A cewarsa, kasuwancin wayoyin GSM ya fara ne daga kasuwar Post Office, kafin daga bisani ya bazu zuwa Farm Centre, Bata, Alkhairat, ‘Yan Kura da sauran manyan kasuwanni a jihar.
“A da matashi idan ya kammala karatu sai ya zauna yana jiran aikin gwamnati. Amma zuwan sana’ar GSM ya sauya wannan tunani. Yanzu akwai masu gyaran waya, masu sayar da sabbin wayoyi, masu sayar da wayoyin London used, da kuma masu sayar da kayan haɗi irin su caji, kebul da sauran kayayyakin gyaran waya,” in ji shi.
Sai dai ya ce babban ƙalubalen da suke fuskanta shi ne yadda ake kawo wayoyin da aka sace domin sayarwa a kasuwa.
Ya bayyana cewa a wasu lokuta mutum kan sayi waya ba tare da sanin cewa sata aka yi mata ba, daga baya kuma jami’an tsaro su kama shi.
“Saboda haka, a matsayina na ɗaya daga cikin shugabannin kasuwa, muna ci gaba da wayar da kan ‘yan kasuwa. Muna da ƙa’ida a kasuwa cewa ba a sayen waya ba tare da rasit ba. Haka kuma ba a sayar da waya ba tare da kwalinta ba, sai dai wasu nau’ikan wayoyi da ba sa zuwa da kwali.
“Idan kuma ba ka san mai sayar da wayar ba, ko kuma ba ka san inda yake ba, bai kamata ka saya a hannunsa ba. Sai dai idan yana da wanda zai tsaya masa (guarantor) da aka sani, domin idan wata matsala ta taso, a samu wanda za a nema,” in ji Malam Auwal.







