Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sunusi II Ya Naɗa Alhaji Sa’ad Ibrahim Ahmad A Matsayin Mayanan Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sunusi II, ya naɗa sabbin masu sarauta a fadarsa ranar Juma’a, ciki har da Alhaji Sa’ad Ibrahim Ahmad wanda aka naɗa a matsayin Mayanan Kano.

Bikin naɗin ya samu halartar ɗimbin jama’a da suka haɗa da ’yan uwa, abokan arziƙi da sauran al’umma daga sassa daban-daban na Jihar Kano da ma wajenta.

Masu halartar sun taya sabon Mayanan Kano murna tare da yi masa addu’ar Allah Ya ba shi ikon sauke nauyin da aka ɗora masa.

Da take magana bayan bikin, mai ɗakin Mayanan Kano, Dakta Asma’u Baba Ɗanbaffa, ƙwararriyar likitar yara a Asibitin Tarayya da ke Abuja, ta gode wa Mai Martaba Sarkin Kano bisa wannan karamci da amincewar da ya yi wajen ba wa mijinta sarautar.

Ta bayyana mijinta a matsayin mutum mai kyawawan halaye, mai taimakon al’umma da tausayin marasa ƙarfi.


“Ba ya nuna bambanci tsakanin talaka da mai arziki. Yana mu’amala da ma’aikatansa cikin mutuntawa, girmamawa da amana. Har ma suna cin abinci tare ba tare da nuna isa ko fifiko ba,” in ji ta.

Dakta Asma’u ta ƙara da cewa Mayanan Kano ya kasance mai taimaka wa masu buƙata gwargwadon ikonsa.
“Duk wanda ya zo gare shi da wata buƙata, yana ƙoƙarin ganin ya samu tallafin da zai rage masa wahala,” ta ce.

Ta jaddada goyon bayanta ga mijinta wajen sauke nauyin da Masarautar Kano ta ɗora masa.
“A matsayina na mai ɗakinsa, ina tare da shi a kowane lokaci kuma ina ƙarfafa masa gwiwa. Na yi farin ciki da wannan naɗi domin mutum ne da ya taso cikin tsarin sarauta kuma yana girmama al’adu da martabar masarauta,” in ji ta.

Ta kuma yi addu’ar Allah Ya ba sabon Mayanan Kano hikima, jagoranci da nasara wajen gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansa.
A wani ɓangare kuma, Dakta Asma’u ta bayyana cewa domin murnar naɗin sarautar, sun gudanar da duba lafiyar yara kyauta tare da wayar da kan iyaye kan muhimmancin rigakafi da hanyoyin kariya daga cututtukan yara a Kofar Fadar Sarki.

Ta ce sun kuma raba magungunan zazzaɓin cizon sauro da sauran magungunan yara kyauta ga waɗanda suka amfana da shirin.
“Za mu ci gaba da gudanar da irin waɗannan ayyukan jin kai domin tallafa wa al’umma da kuma inganta rayuwarsu. A matsayina na mace, zan ci gaba da bai wa mijina duk wani goyon baya da ya dace wajen hidimtawa jama’a,” in ji Dakta Asma’u.

A nasa jawabin, sabon Mayanan Kano, Alhaji Sa’ad Ibrahim Ahmad, ya gode wa Masarautar Kano ƙarƙashin jagorancin Khalifa Muhammad Sunusi II bisa wannan karramawa da ta yi masa da kuma zuriyar Matawalle ta hanyar ba shi wannan sarauta.

Ya ce zai ci gaba da nuna biyayya da girmamawa ga Masarautar Kano, tare da kare martabarta da mutuncinta a kowane lokaci.

Haka kuma, ya gode wa dukkan waɗanda suka halarci bikin da kuma waɗanda suka taya shi murnar wannan naɗi, yana mai addu’ar Allah Ya saka musu da alheri.

  • Related Posts

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2027 mai kimanin Naira Tiriliyan 1.107 ga Majalisar Dokokin jihar Kano, inda ya…

    Takarar Majalisar Jaha Da Nake A ADP Amsa Kiran Al’ummar Gwale Ne -Dakta Bashir Aliyu Galadanci

    Dag Ibrahim Muhammad Kano Dan takarar majalisar dokokin Jihar Kano a Karamar Hukumar Gwale a jam’iyyar ADP, Dakta Bashir Aliyu Galadanci, ya bayyana cewa al’ummar karamar hukumar ne suka matsa…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo