Daga Ibrahim Muhammad Kano.
Kwalejin Islamiyya da Ilimin Zamani ta Zam-Zam da ke jihar Kano ta gudanar da bikin saukar haddar Alkur’ani mai girma karo na hudu tare da yaye dalibai da raba kyautuka. An gudanar da taron ne ranar Asabar 1/8/26 a harabar makarantar.
Da yake jawabi a taron, Jagoran Makarantar kuma Shugaban Hukumar Hisba na Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana farin cikinsa bisa nasarorin da kwalejin ke samu. Ya ce an kafa kwalejin ne a shekarar 2017, kuma tana ba da ilimin addini da na zamani mai inganci tare da dora dalibai kan kyakyawar tarbiyya.
Sheikh Daurawa ya ce kwalejin tana samun dalibai daga ciki da wajen kasar nan. Ya kara da cewa daliban da suka kammala a kwalejin yanzu suna karatu a manyan jami’o’i daban-daban a cikin gida da waje. “Nan gaba da wuya a je wani wuri na aiki ba tare da an sami ɗalibin Zam-Zam ba,” inji shi. Ya bayyana cewa yanzu haka suna da ɗalibai mata sama da 100 da ke karatun fannin lafiya a jami’o’i daban-daban.
Jagoran ya yaba wa malaman kwalejin bisa jajircewa da sadaukarwa da suke nunawa, inda mafi yawansu mahaddata ne kuma masu ilimin zamani. Ya kuma yi kira ga iyaye da su cigaba da ba da hadin kai ta hanyar biyan kudaden makaranta a kan lokaci domin karfafa wa makarantar gwiwa.
Sheikh Daurawa ya kara yin kira ga dalibai da su cigaba da hazaka da juriya wajen neman ilimi. Ya bayyana fatan cewa nan gaba kwalejin za ta kai matakin kafa jami’a, tare da rokon Allah ya sakawa duk wanda ya bayar da gudunmawa ga makarantar da mafificin alheri.
A jawabinsa, Darakta Janar na Kwalejin Zam, Malam Usama Aminu Ibrahim ya ce manufar makarantar ita ce samar da mahaddata Alkur’ani masu aiki da shi, masu ilimin rayuwa, da samar da ‘yan kasa nagari wadanda za su taimaka wajen cigaban al’umma a fannoni daban-daban.
Malam Usama ya bayyana cewa daliban da suka yaye sun hada da masu haddar juzu’i 10, masu haddar juzu’i 30, da wadanda suka kammala makarantan guda 6. Ya kuma ce domin inganta sadarwa da iyaye, makarantar ta samar da manhajar sadarwa ta zamani “Portal” domin sanar da iyaye abubuwan da suka shafi makaranta da dalibai.
A yayin taron, an kaddamar da mujallar makarantar. Daga cikin wadanda suka kaddamar akwai Alhaji Sabitu Ahmad Usman Kazaure wanda ya sayi kwafi daya da N200,000, da kuma Injiniya Muhammad Kabir Salisu wanda ya sayi kwafi 3 akan N200,000.
Haka zalika daliban sun nuna hazaka ta hanyar kera kayayyaki da suka hada da jirgin kasa da matatar ruwa da sauran na’urori.
Daga cikin manyan baki da suka halarta akwai Farfesa Sa’id Yunusa da Mujahid Aminuddeen Mataimakin Kwamandan Hisba na Jihar Kano, tare da dinbin iyaye da malamai.








