Hajiya Hauwa Nuhu Wali: Za Mu Yi Aiki Tuƙuru Don Tabbatar Da Nasarar Gwamna Abba A 2027

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Sabuwar Sakatariyar Dindindin a Ma’aikatar Al’amuran Addini ta Jihar Kano, Hajiya Hauwa Nuhu Wali, ta bayyana godiyarta ga Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Gwani Ali Haruna Makoɗa, da dukkan ma’aikatan ma’aikatar bisa goyon bayan da suka ba ta a dukkan muƙaman da ta riƙe, har zuwa lokacin da ta zama Darakta a Kwalejin ’Yan Mata ta Dala, kafin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada ta a matsayin Sakatariyar Dindindin.

Hajiya Hauwa ta bayyana jin daɗinta bisa irin karɓar da Kwamishinan Ilimi da ma’aikatan ma’aikatar suka yi mata, da kuma addu’o’in da suka yi mata a lokacin da take miƙa aiki.

Haka zalika, ta ce ma’aikatan Ma’aikatar Al’amuran Addini da aka tura ta sun karɓe ta hannu biyu-biyu, tare da yi mata alƙawarin ba ta cikakken goyon baya da haɗin kai.

Sabuwar Sakatariyar ta yi musu albishir da cewa za su yi aiki tare domin tabbatar da nasarar gwamnati, tana mai cewa ƙofar ofishinta a buɗe take ga duk wanda zai bayar da shawara mai amfani ga al’umma.

Ta ce hakan zai taimaka wajen cimma manufofin Gwamnatin Kano, da kuma tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf domin sake samun nasara a zaɓen 2027.

Hajiya Hauwa ta yi kira ga dukkan Sakatarorin Dindindin da ma’aikata da su yi aiki tukuru domin samun nasarar Gwamna Abba, tana mai cewa wannan shi ne sakayyar da za su yi masa bisa kulawa da yake ba su.

Ta kuma tunatar da cewa duk inda ta yi aiki, malamai da suke aiki tare da ita, musamman a GGC Dala, su ne suka kasance abokan shawararta.

“Idan ba da su ba, aiki ba zai tafi ba. Duk nasarar da na samu tasu ce, saboda irin goyon bayan da suka ba ni,” in ji ta.

Ta buƙaci waɗanda suka yi aiki tare da ita, kuma suke nuna damuwa kan rabuwar da za su yi, da su yi haƙuri, tana cewa: “Haka aiki ya gada. Abin da zan ce shi ne, Allah ya saka da alheri, ya kuma ɗaukaka matsayinsu.”

Hajiya Hauwa ta ce ba za ta taɓa mantawa da Hukumar Kula da Makarantun Sakandare ta Jihar Kano, Dala Zonal Office, PTA, Tsofaffin Daliban GGC Dala, da sauran ƙungiyoyi, da kuma al’ummar Gwammaja da ke makwabtaka da GGC Dala ba, bisa irin haɗin kai da goyon bayan da suka ba ta.

A ƙarshe, sabuwar Sakatariyar ta yi jinjina da godiya ga mai gidanta, wanda ta ce da goyon bayansa da taimakonsa ne ta kai ga wannan matsayi. Ta bayyana shi a matsayin uba, aboki, yaya da ɗan’uwa gare ta.

Haka zalika, ta yaba da irin kulawar da zuriyarta, da na Yusuf Ɗan Majwayo da na Ustaz Umar, suke ba ta, tare da addu’ar Allah ya saka wa dukkan iyalanta da alheri.

  • Related Posts

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Sakamakon irin dimbin alheri da gudummawar da dan takarar majalisar tarayya na PDP, Hon. Alhaji Abubakar Ibrahim Maina, ke bai wa al’ummar karamar hukumar Tarauni, al’ummar…

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo