Daga Ibrahim Muhammad Kano
Mai ba Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, shawara kan ci gaban matasa da wasanni, Hon. Sani Musa Danja, ya bayyana cewa amincewa da gaskiya da riƙon amana da Gwamnan Kano ya yi ne suka sa aka kawo shirin tallafin matasa na Gwamnatin Tarayya, “YEIDEP’s Financial Partners”, zuwa Jihar Kano.
Hon. Danja ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a lokacin ƙaddamar da rabon takardun buɗe asusun banki ga masu cin gajiyar shirin. An gudanar da taron ne a zauren wasanni na Sani Abacha da ke Kofar Mata, Kano.
Hon. Sani Musa Danja, wanda shi ne Shugaban Shirin “YEIDEP’s Financial Partners” na jihohin Arewa, ya ce yadda jama’a suka yi ta tururuwa domin rungumar shirin shaida ce ta irin amincewar da suke da ita cewa duk wanda ya samu damar cin gajiyarsa zai amfana ba tare da wata matsala ba.
“Saboda amana da mutane ke da ita ga Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya sa suka yi imani cewa shirin zai bi tsari,” in ji shi.
Ya ce shirin na Gwamnatin Tarayya ne da nufin tallafa wa ’yan ƙasa ta hanyar samar musu da jari. Ya bayyana cewa ba koyaushe ake magance matsalar tashin hankali ta hanyar amfani da jami’an tsaro da bindiga ba, domin a wasu lokuta koyar da sana’a, samar da ayyukan yi da ba da jari na iya zama mafita mai inganci wajen hana aikata laifuka da tashin hankali.
A cewarsa, wannan ita ce babbar manufar shirin, wato hana matasa shiga ayyukan tashin hankali ta hanyar samar musu da sana’o’i da hanyoyin dogaro da kai.
“Idan mutum yana zaune ba shi da abin da zai ci ko ya sha saboda rashin sana’a, yunwa na iya kai shi ga aikata abin da bai dace ba. Shi ya sa muke son matasa da yawa su amfana da shirin,” in ji shi.
Hon. Danja ya bayyana cewa Jihar Kano kaɗai ta samu kaso na matasa miliyan ɗaya da za su amfana da shirin. Ya ce suna godiya ga Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bisa amincewa da gudanar da shirin, sannan ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa gudummawar da ya bayar wajen tabbatar da cewa al’ummar Jihar Kano sun amfana.
Ya ƙara da cewa za a gudanar da shirin mataki-mataki, inda a matakin farko matasa 100,000 za su fara amfana.
Ya ce duk wanda ya halarci taron ya bayar da sunansa da bayanansa, za a fara da su wajen rabon tallafin, domin tabbatar da adalci da bin tsari.








