NDC Kano: Gawuna Yana Nan Daram, Bai Da Shirin Barin Jam’iyya -Mairiga

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Shugaban Jam’iyyar National Democratic Congress (NDC) na Jihar Kano, Hon. Husaini Isah Mairiga, ya bayyana cewa tsohon ɗan takarar Gwamnan Kano, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna, yana nan daram a cikin jam’iyyar, inda yake neman kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya a ƙarƙashin NDC.

Mairiga ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano, inda ya ce, duk da cewa wasu daga cikin muhimman amintattun Gawuna na siyasa an gan su suna ganawa da Gwamnan Kano tare da shirin komawa jam’iyyar APC, hakan ba yana nufin Gawuna ma zai bar NDC ba.

Ya ce mutanen da ake magana a kansu sun kasance abokan tafiyar siyasar Gawuna tun zamanin tsohuwar jam’iyyar ANPP, inda suka yi aiki tare a mukamai daban-daban da ya rike, har zuwa lokacin da ya tsaya takarar Gwamnan Kano a ƙarƙashin APC.

“Wasu daga cikinsu ’yan Gawuna ne da suka yi siyasa tare da shi har zuwa lokacin da ya fice daga APC ya koma ADC tare da su. Haka ma lokacin da ya koma NDC, sun biyo shi,” in ji Mairiga.

Shugaban NDC na Kano ya ce daga baya wasu daga cikin mutanen sun fara korafin cewa Gawuna ya koma ADC, sannan ya koma NDC ba tare da ya tuntube su ba, tare da cewa ba ya ba su wata makoma a cikin jam’iyyar. Ya ce saboda haka ne aka zauna da su aka tattauna batun, inda aka cimma matsayar cewa za su gana da jagoran siyasar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, domin a shawo kan matsalar.

“Sai dai tun daga lokacin bai sake ganinsu ba. Abin mamaki yanzu na ga sun fito a hoto suna ganawa da Gwamnan Kano, suna shirin komawa APC,” in ji shi.

Mairiga ya ce yana ganin wataƙila suna da wata bukata a wajen gwamnati ne ya sa suke tunanin komawa APC, yana mai cewa da sun yi haƙuri suka ci gaba da zama a NDC, da yardar Allah, idan jam’iyyar ta samu nasara a zaɓen 2027, za a samar musu da kyakkyawar makoma a cikin jam’iyyar.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum