Daga Ibrahim Muhammad Kano
Jam’iyyar PDP a Jihar Kano ta bayyana cewa taron da jam’iyyar APC ta gudanar a jihar ba zai tsoratar da ita ba, tana mai cewa ba za ta ji tsoron irin wannan taron ba.
Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar PDP a Jihar Kano, Kwamared Ahmad Dauda Lawan, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce an tilasta wa al’ummar Jihar Kano rayuwa cikin talauci, saboda haka idan aka fito da kuɗi, kowa zai karɓa ya halarci taro, amma ranar zaɓe kowa zai yi abin da ya dace.
“Ba ya kamata a ci gaba da ɗaukar kuɗin al’ummar Jihar Kano ana yin tarukan siyasa da su ba. Domin mu ma ’yan PDP muna da haƙƙi, saboda mu ma ’yan Kano ne,” in ji shi.
Kwamared Ahmad ya ce duk lokacin da PDP za ta gudanar da taro, ita ma za ta rubuta wa Gwamnatin Jihar Kano takarda ta ba ta kuɗi domin gudanar da taron, saboda tana da haƙƙin hakan.
Ya ce, “Idan kuma ba a ba mu ba, to Gwamna ya yi zalunci, kuma ya karya rantsuwar da ya yi da Alƙur’ani cewa zai yi wa kowa adalci.”






