Dattawan Kano Masu Katin Zaɓe Sun Yi Taro Domin Tattauna Nasarar Atiku a 2027

Daga Ibrahim Muhammad Kano

An gudanar da wani taro na dattawan Kano masu katin zaɓe, waɗanda ke goyon bayan takarar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, domin tattauna hanyoyin samun nasararsa a zaɓen 2027.

An gudanar da taron ne ƙarƙashin Ofishin Mataimaki na Musamman kan Hulɗa da Masu Ɗauke da Katin Zaɓe da Tsara Ayyukan Masoya Atiku na Shiyyar Arewa maso Yamma, Kwamared Idris Ibrahim Unguwar Gini.

A jawabinsa, Kwamared Unguwar Gini ya ce manufar taron ita ce sauya salon siyasar da ake yi, tare da bai wa abubuwan da suka dace da muhimmanci a cikin tsarin siyasa.

“Duk wani abu da yake da daraja, muna so ya shiga cikin tsarin siyasa,” in ji shi.

Ya ce duk ɗan asali da ya yarda cewa nasarar rayuwa tana tare da biyayyar iyaye, ya kamata ya ba dattijai da iyaye hakkinsu da darajarsu.

“A matsayina na mai riƙe da Ofishin Mataimakin Wazirin Adamawa, mahadar farko da za mu fara don nasarar Atiku ita ce mu kula da iyaye. Su mallaki ’ya’yansu, dattijai su mallaki zuriyarsu. Mu daina barin wasu ’yan siyasa suna zuwa suna raba taliya da ’yan kuɗi, su sa matasa da matansu su fito su zaɓi abin da zai zama masifa,” in ji shi.

Kwamared Unguwar Gini ya ƙara da cewa barin yara su yi abin da suka ga dama ba tare da iyaye sun ba su shawara ba na iya haifar da illa ga al’umma.

“Shi ya sa ’yan siyasa ke mayar da yara ’yan ƙwaya da jagaliya. Suna ba su kuɗi, suna yaudararsu da ba su babura, idan sun ci sai su jawowa al’umma masifa. Iyaye ne ya kamata su koya wa ’ya’yansu abin da ya dace,” in ji shi.

Ya ce al’ummar Najeriya da kansu ne ya kamata su yanke shawarar wanda za su zaɓa a 2027, ba wai su jira wani ya yi musu yaƙin neman zaɓe ba.

“Su ne za su ga ya kamata su kayar da Tinubu, kuma Atiku Abubakar shi ne zai iya. Mataki na farko shi ne kada Tinubu ya tabbata, sannan sauran komai zai biyo baya,” in ji shi.

Dangane da batun tallafin man fetur, Kwamared Unguwar Gini ya ce shirin da Atiku ya bayyana na dawo da tallafin ba zai kasance abin da ba za a iya aiwatarwa ba.

“Domin waɗanda suka cire tallafin sun san sun tattara dukiya. Har yanzu suna ba wa kansu tallafin man fetur. Dama su ne masu rijiyoyin mai, su ne ke fitarwa, su kuma ke shigo da shi,” in ji shi.

Ya kuma yi gargadin cewa idan aka sake zaɓar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, farashin litar fetur na iya kai wa naira 5,000.

Kwamared Idris Ibrahim Unguwar Gini ya bayyana gamsuwarsa da yadda taron ya gudana, yana mai cewa taron dattawan Kano masu goyon bayan nasarar Atiku ne, kuma mahalarta sun zo ne da kansu saboda kishin ƙasa da son ganin an samu sauyi.

“Ba wanda aka ba kuɗi. Muna fatan za mu yi aiki tukuru wajen ɗora ’ya’ya da iyalai a kan yin abin da ya dace domin samun nasarar Atiku a 2027,” in ji shi.

Shi ma Shugaban Ƙungiyoyin Yaƙin Neman Zaɓen Atiku Abubakar daga 2023 zuwa yau, Alhaji Kabir Abubakar Babawo, ya bayyana farin cikinsa da yadda taron ya gudana.

“Ba a taɓa ganin irin wannan taro a Kano ba. Iyaye da kakanni masu shekaru 60, 70 da 80 sun halarta. Wannan ya tabbatar mana cewa mun sami mutanen da za su kare mana ƙuri’un Atiku. Idan ka ga fuskokin irin waɗannan dattijai a bakin akwatin zaɓe, ba za ka iya yin rashin kunya ba,” in ji shi.

Ya ce Atiku Abubakar mutum ne da ya san darajar mutane, ba mai raini ko wulakanci ba, yana mai bayyana shi a matsayin mutum mai magana ɗaya kuma mai iya amincewa da kuskurensa tare da gyara.

“Shugaban ƙasa ya zo ya cire tallafi, ana wahala, amma yana bakin ciki. Atiku zai dawo da tallafi domin mutane su sami sauƙin rayuwa,” in ji shi.

Alhaji Babawo ya ce suna kallon zaɓen 2027 a matsayin zaɓen da za su samu nasara, inda ya yi kira ga jama’a da su fito su yi amfani da ƙuri’unsu domin kawo adalci da kawo ƙarshen zalunci, kisan kai da rashin tsaro.

A nasa jawabin, Mataimaki na Musamman ga Atiku Abubakar kan Masu Ruwa da Tsaki da Tsare-tsare, Farfesa Ahmad Shehu, ya bayyana farin cikinsa da ganin dattijai da dama sun halarci taron.

Ya ce a lokacin da Atiku Abubakar yake Mataimakin Shugaban Ƙasa daga 1999 zuwa 2007, Najeriya ta samu ci gaba a fannonin tattalin arziki, zaman lafiya da ilimi.

“Atiku shi ne zai magance matsalolin da suka addabi al’umma. Babu wani da yake nuna rashin ƙabilanci a ƙasar nan kamar Atiku. Ya ɗauki kansa ɗan Najeriya ne,” in ji Farfesa Ahmad Shehu.

A nasa jawabin, dattijon ɗan siyasa, Alhaji Sulayman Mambo, ya ce dattawa ba za su bari a ci gaba da yin abin da aka ga dama da matasa da yara ba.

“Hakkinsu ne dattawa. Ba za mu ƙyale a riƙa yin abin da aka ga dama da yara ba. Daga wannan taro muna tabbatar wa kowane ɗan siyasa a Kano ya shiga taitayinsa. Ba za mu bari a lalata Kano ba. Kano ta wuce garin wani. Duk Yammacin Afirka babu wanda ba shi da wakili a Kano. Idan Kano ta lalace, za ta shafi Afirka baki ɗaya,” in ji shi.

Ya ce abubuwa biyu ne suka fi damun al’umma a halin yanzu, wato talauci da rashin tsaro.

“Allah Ya kiyaye mu da rashi da yunwa, Ya kuma cire mana tsoro. Wannan shi ne abin da duk wani shugaba na Najeriya ya kamata ya yi yanzu. Duk inda talauci yake, yunwa na nan. Duk inda yunwa da tashin hankali suke, akwai tsoro. Mu muna burin a kawar da su,” in ji shi.

  • Related Posts

    ADC Ce Mafita Ga Jihar Kano -Hon. Musaddik Tofa

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Ɗan takarar majalisar tarayya na jam’iyyar ADC mai wakiltar ƙananan hukumomin Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado, Hon. Musaddik Bashir Usman Tofa, ya bayyana cewa jam’iyyar…

    Babu Wani Sauyi A ’Yan Takarar NDC Na Kano — Kwankwaso

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jagoran Kwankwasiya kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta samun wani sauyi a jerin ’yan takarar jam’iyyar…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

    Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

    ADC Ce Mafita Ga Jihar Kano -Hon. Musaddik Tofa

    ADC Ce Mafita Ga Jihar Kano -Hon. Musaddik Tofa

    Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

    Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

    Ba zai yiwu ka goyi bayan APC da wasu jam’iyyu a lokaci guda ba — Dauda Lawal ga Wike

    Ba zai yiwu ka goyi bayan APC da wasu jam’iyyu a lokaci guda ba — Dauda Lawal ga Wike

    ZAMFARA: A Wata Mai Zuwa Jirgin Sama Zai Fara Jigilar Fasinjoji Tsakanin Gusau Da Abuja

    ZAMFARA: A Wata Mai Zuwa Jirgin Sama Zai Fara Jigilar Fasinjoji Tsakanin Gusau Da Abuja

    Ana Gudanar Da Bita Ga Ƙwararrun Masu Maganin Gargajya a Jihar Kano

    Ana Gudanar Da Bita Ga Ƙwararrun Masu Maganin Gargajya a Jihar Kano