Shugaban Fagge Ya Bai Wa Mata 180 Tallafin Jari, Ya Raba Babura Ga Kansiloli

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Fagge, Hon. Usman Salisu Masu, ya bai wa mata 180 tallafin jari na N50,000 kowacce, a wani ɓangare na ci gaba da shirin tallafa wa mata da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke gudanarwa a ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.

An gudanar da rabon tallafin ne a harabar sakatariyar ƙaramar hukumar ranar Litinin, inda kowacce daga cikin matan da suka amfana ta karɓi kuɗinta a hannu nan take.

A yayin taron, shugaban ƙaramar hukumar ya gargadi matan da kada su bayar da wani kaso na kuɗin tallafin ga duk wanda zai zo ya ce shi ne ya sanya sunansu cikin waɗanda za su amfana. Ya ce, sai dai idan mace tana son yin ihsani da kanta, za ta iya tallafa wa wasu bisa ga yadda ta ga dama.

Ya bayyana cewa rabon tallafin, wanda aka gudanar sau da dama a ƙaramar hukumar, wani ɓangare ne na cika alkawarin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka tun kafin zuwansa mulki na tallafa wa mata da jari. Ya ƙara da cewa a halin yanzu, mata da dama a Fagge sun riga sun amfana da tallafin, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kai shi ga sauran waɗanda ba su samu ba.

Hon. Masu ya yi kira ga al’ummar Fagge da su ci gaba da bai wa gwamnatin jihar Kano goyon baya a zaɓe mai zuwa, domin dorewar ayyukan ci gaba da yankin ke amfana da su a ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, musamman a fannonin ilimi da bunƙasa rayuwar al’umma.

Ya kuma bayyana wasu daga cikin ayyukan da ya gudanar a ƙaramar hukumar tun bayan hawansa kan mulki, musamman a fannin ilimi, tallafa wa ci gaban al’umma da sauran ayyukan raya ƙasa.

Shugaban ya yi kira ga al’ummar Fagge da su zaɓi jam’iyyar APC a kowane mataki, yana mai cewa nasarar jam’iyyar za ta taimaka wajen ci gaba da ayyukan da gwamnatin jihar ke gudanarwa.

A yayin taron, Hon. Masu ya raba babura ga zaɓaɓɓun kansiloli, naɗaɗɗun kansiloli, wasu ma’aikata da sakataren ilimi na ƙaramar hukumar, domin sauƙaƙa musu sufuri. Haka kuma, ya bai wa masu ba shi shawara da mataimakansa na musamman tallafin N200,000 kowanne.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo