Daga Ibrahim Muhammad Kano.
Ɗan kasuwa a jihar Kano Alhaji Hamisu Rabi’u Jingau ya bayyana cewa za su ɗaura ɗamara domin tabbatar da cewa duk wanda yake tare da su kuma suke aiki a ƙarƙashinsa, kowa ya mallaki nasa hannun jarin matatar man Ɗangote da izinin Allah.
Ya ce, sauran al’umma ma su karɓi wannan dama hannu biyu-biyu, domin wata dama ce ta musamman da idan ta wuce, ba lallai ba ne a sake samunta. Dama ce da ta zo wa ‘yan Najeriya.
Don haka, a maimakon matasa su riƙa kashe kuɗi wajen sayen manyan wayoyi da sabbin babura da kuma sayen kaya na ado da ba dole ba, ya kamata su tattara kuɗaɗen su sayi hannun jari a matatar man Ɗangote, domin zai amfanar da su nan gaba.








