Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya raba sabbin motocin aiki ga manyan makarantun gaba da sakandare da wasu hukumomin ilimi na jihar, a wani mataki da ya ce zai ƙara inganta ayyuka da tafiyar da harkokin ilimi.

An gudanar da rabon motocin ne ranar Juma’a a Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara da ke Gusau, babban birnin jihar.

A cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce motocin mallakar hukumomi ne, kuma za a yi amfani da su wajen gudanar da harkokin gudanarwa da ayyuka, sa ido kan ayyuka, tantance makarantu, halartar ayyukan hukuma da sauran nauyin da ya rataya kan cibiyoyin da suka amfana.

Cibiyoyin da aka ware wa sabbin motocin sun haɗa da Jami’ar Tarayya ta Gusau, Jami’ar Jihar Zamfara da ke Talata Mafara, da Kwalejin Fasaha ta Abdu Gusau da ke Talata Mafara.

Sauran waɗanda suka amfana sun haɗa da Kwalejin Koyar da Aikin Jinya da Ungozoma ta Gusau, Hukumar Kula da Ayyukan Malamai, Hukumar Kula da Makarantun Sakandare, Sashen Tabbatar da Ingancin Ilimi, Kwalejin Nazarin Larabci da Shari’a ta Zamfara (ZACAS), da sauran cibiyoyin gwamnati na jihar.

Da yake jawabi yayin rabon motocin, Gwamna Lawal ya ce matakin zai taimaka wajen ƙara ƙwazo da ingancin ayyukan jami’an gwamnati, musamman ta hanyar samar musu da hanyoyin sufuri masu inganci da za su ba su damar gudanar da ayyukansu cikin sauri da sauƙi.

Gwamnan ya jaddada cewa motocin ba mallakar kowane jami’in gwamnati ba ne, sai dai dukiyoyin Gwamnatin Jihar Zamfara ne da aka bayar domin ayyukan hukuma.

Ya ce, “Ya kamata a fahimci cewa waɗannan motocin ba wani haƙƙi ne na ƙashin kai da wani jami’in gwamnati zai mallaka ba. Dukiyoyin Gwamnatin Jihar Zamfara ne, kuma dole ne a yi amfani da su yadda ya kamata, musamman wajen gudanar da ayyukan hukuma kawai.

“Ina sa ran cibiyoyin da suka karɓi motocin za su ɗauki cikakken alhakin kula da su, yadda ake amfani da su, gyaransu da kuma adana bayanan da suka shafe su. Shugabannin cibiyoyin za su ɗauki alhakin duk wata ɓarna, amfani da su ba bisa ƙa’ida ba ko kuma lalacewar da za a iya kauce mata.

“Yayin da gwamnati ke ƙara zuba jari a fannin ilimi, dole ne mu gina al’adar kula da dukiyar gwamnati da ɗaukar alhaki. Ya kamata dukiyar jama’a ta ci gaba da amfani ga jama’a har tsawon lokacin da aka tanade ta.

“Dole ne mu himmatu wajen samar da ingantaccen tsarin gudanar da aiki, tare da ba da muhimmanci ga gaskiya, riƙon amana da ɗaukar alhaki.

“Gwamnatina za ta ci gaba da samar da gine-gine, kayan aiki da sauran tallafin da cibiyoyin ilimi ke buƙata domin inganta ilimin gaba da sakandare a Zamfara. A madadin haka, muna sa ran samun shugabanci nagari, gudanar da dukiya cikin taka-tsantsan, da kuma ingantattun sakamako a fannin karatu da gudanar da harkokin makarantu.”

Gwamna Lawal ya kuma taya cibiyoyin da suka amfana murna, tare da buƙatarsu da su tabbatar da cewa motocin sun amfani cibiyoyin, ɗalibai da al’ummar Jihar Zamfara baki ɗaya, maimakon amfani da su wajen biyan buƙatun wasu mutane na ƙashin kansu.

Related Posts

Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Makarantar Africa Academy, wadda ke gudanar da karatu ta yanar gizo ƙarƙashin Africa TV3, ta gudanar da bikin yaye dalibai 3,500 da suka kammala karatun Diploma…

Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Sha’awar ganin an sauya mummunan kallon da al’umma ke yi wa masu maganin gargajiya ce ta sanya Wazirin Magani na jihar Kano, Alhaji Nasiru Sani Abubakar,…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

ADC Ce Mafita Ga Jihar Kano -Hon. Musaddik Tofa

ADC Ce Mafita Ga Jihar Kano -Hon. Musaddik Tofa

Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

Ba zai yiwu ka goyi bayan APC da wasu jam’iyyu a lokaci guda ba — Dauda Lawal ga Wike

Ba zai yiwu ka goyi bayan APC da wasu jam’iyyu a lokaci guda ba — Dauda Lawal ga Wike

ZAMFARA: A Wata Mai Zuwa Jirgin Sama Zai Fara Jigilar Fasinjoji Tsakanin Gusau Da Abuja

ZAMFARA: A Wata Mai Zuwa Jirgin Sama Zai Fara Jigilar Fasinjoji Tsakanin Gusau Da Abuja

Ana Gudanar Da Bita Ga Ƙwararrun Masu Maganin Gargajya a Jihar Kano

Ana Gudanar Da Bita Ga Ƙwararrun Masu Maganin Gargajya a Jihar Kano