Muna Da Kyakyawan Zaton Shigowar Jigajigan Mutane Jam’iyyar ADC Za Ta Samar Da Nasara Ga Al’umma -Amb. Mai Nasara Salga

Daga Wakilinmu.

A yayin da jam’iyyar ADC take ci gaba da samun karbuwa da samun shigowar muhimman mutane manyan jagororin siyasa cikinta daga jam’iyyu daban daban. jigo a cikin jam’iyyar da ya dade yana bada gudummuwa wajen bunkasata a jihar Kano daga karamar hukumar Dala.Ambasada Abdulrahman Mai nasara Salga ya bayyana jin dadinsa da yanda jam’iyyar take samun karbuwa.

Ambasada Abdulrahman Salga da ya yi takarar neman dan majalisar tarayya a karamar hukumar Dala a 2023. yace abin farin ciki ne gare su irin bunkasa da ake samu a jam’iyyar da suka jima suna kokarin ganin ta karbu ta tallata manufofinta a tsakanin jama’a da yanzu tana karbuwa a tsakanin al’umma za ta zama tudun mun tsira ga duk mai son ganin an samar da shugabanci nagari a kasarnan.

Abdulrahman Salga da ya dade yana bada gudummuwa na ganin ADC ta karbu tun daga tushe ya samar da ofishin jam’iyyar a Dala da yin banoni da riguna da huluna da kuma tallata jam’iyyar ta bangarori daban daban yace shigowar Dakta Rabiu Musa jagoran Kwankwasiyya da dinbin magoya bayansa tare da shigowar tsohon mataimakin Gwamnan Kano kwamared Aminu Abdulsalam da dan takarar Gwamnan Kano a jam’iyyar APC a zaben 2023 .Dakta Nasir Yusuf Gawuna jam’iyyar ADC a nan Kano babban ci gaba ne da nasara ga jam’iyyar da ake ganinta karama ce a baya yanzu ta zama jam’iyyar adawa mafi karfi a kasar nan.

Ambasada Abdulrahman Salga ya ce shigowar manyan jiga jigai jam’iyyar a jihar Kano suna da kyakkyawar zaton za ayi adalci a ciki da kafa shugabanci mai kyau a jihar Kano da kuma Nijeriya baki daya.
Abdulrahman mai nasara yace su a matsayinsu na.yan jam’iyyar za.su cigaba da abinda suke na ganin al’umma sun karbe ta suna fata jiga jigan shugabanni da suke a jam’iyyar tun daga kan tsohon mataimakin shugaban kasa.Atiku Abubakar da Obi da Kwankwaso da sauran jagorori zasu hada kai asa mafitar kasarnan a gaba domin kaiwa ga nasara a zaben 2027 mai zuwa.

  • Related Posts

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Hon Alhaji Bashir Abubakar Galadima, hadimin Gwamnan jihar Kano a ma’aikatar kananan hukumomi, ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka kammala gyare-gyaren kasafin kudin shekarar 2027…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength