Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana shekaru biyu na mulkin Bola Ahmad Tunibu a matsayin alkhairi ga Kanawa, duk da ba su da gwamnatin jiha, amma sun fi masu gwamnatin walwala.
Hon. Kabiru Ibrahim, tsohon shugaban majalisar kansiloli na ƙaramar hukumar Makoɗa a jam’iyyar APC ne ya bayyana hakan.
Ya ce ko babu komai matamakin shugaban Majalisar Dattawa Sanata Barau I. Jibrin yana abin da ya kamata wajen ɗaukar mutane ya yi aiki da su da shi ma yana daga ma’aikata na ofishinsa wanda ake tallafa masa a kan lura da ayyuka na al’umma kuma salo na zuwa ƙasa da yardar Ubangiji.
Ya ce jagororinsu tun daga kan Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, suna gode musu, suna musu fatan alkhari a kan irin ɗawainiya da suke da jama’a. Ya yi fatan Allah ya saka musu da alkhairi.
Hon. Makoɗa ya yi nuni da cewa mataimakin shugaban majalisar Dattawa na ƙasa, Barau I. Jibrin Jagora ne ɗaya tamkar da miliyoyi duba da irin alkhairai da yake saukewa ga al’umma, ba tare da kallon bambancin jam’iyya ba.
Makoɗa ya ce, idan mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa na ƙasa, Sanata Barau I. Jibrin ya tashi yin abin alheri kallo yake na ina zai kawo wa al’umma cigaba. “Shi ya sa koyaushe muke masa fatan alkhairi. A wannan tsarin idan ya zama Gwamnan jihar Kano za a ga gagarumin cigaba,” in ji shi.






