An Karrama Ƙaramin Ministan Gidaje Ata A Kano

Daga Ibrahim Muhammad Kano

A ƙoƙarinsa na tallafa wa ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar Kano daga tushe, ƙaramin Ministan Gidaje, Hon. Yusuf Abdullahi Ata ya raba wa tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi, mataimakansu da kansiloli zaɓaɓɓu da masu gafaka na ƙananan hukumomi 44 tallafi.

An yi rabon tallafin ne a ranar Litinin a babban ɗakin taro na Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke kan titin Katsina a jihar Kano.

Sai dai rabon ya bar baya da ƙura sakamakon wasu daga tsofaffin kansilolin da masu ba da shawara sun koka da rashin samun tallafin bayan sun baro ƙananan hukuminsu na nesa.

Wasu kansilolin sun shaida mana sun zo ne a matsayin wakilci na raguwar kansilolin daga ƙananan hukumominsu, amma sai aka ce wani ya karɓi nasu.

Haka su ma masu ba da shawarar an sami wannan matsalar ta wasu sun karɓi na wasu.

Wani tsohon shugaban kansilolin da ya zo daga wata ƙaramar hukumar ya ce, an soma rabon tallafi kuɗin cikin tsari da yanayi mai kyau, amma daga baya da aka zo kan na kansiloli ne tsarin ya karye, abin da wasu ke ganin kamar da gangan aka yi domin a rikita tsarin.

Sai dai bayan jan lokaci ana tinja-tinja na yadda za a ba da kuɗin tun daga ɗakin da ake taron, sai da aka fito waje aka kusa zagaye harabar bene na ɗaya da aka yi taron don ganin yadda za a shawo kan lamarin.

A ƙarshe an zartar da bai wa kowane mutumin da ya zo wajen.

Sai dai wani tsohon Kansila da shi ma ya zo a matsayin wakilci, zai karɓi na tsofaffin kansilolin yankin su ya ce, shi bai karɓa ba, abin da ya sa kuma bai karɓi kuɗin ba shi ne, ya je taron ne a wakilcin tsofaffin kansilloli na yankinsu, amma sai aka ce shi kaɗai za a bai wa, don haka bai karɓa ba.

Mun yi ƙoƙarin ji daga masu ruwa da tsaki na masu rabon tallafin da suka haɗa da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kano, tsohon dan majalisar jiha, Hon. Salisu Maje Ahmad Gwangwazo da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Fagge, Hon. Ibrahim Abdullahi Shehi, waɗanda suna daga cikin manyan hadiman Ministan, amma ba wanda ya amince muka yi magana da shi.

Wani daga cikin tawagar masu rabon a gefe ya shaida mana cewa, rabon da kyakkyawan manufa aka yi da tsarin da kowa zai samu, amma sai aka sami karyewar tsarin.

Ya ce, duk wanda sunansa ke cikin jerin sunayen tsofaffin kansilolin da masu ba da shawara da shugabannin ƙananan hukumomi da mataimakansu na gwamnatin APC da ta gabata za su samu, ba wanda zai rasa.

A yayin taron, Shugaban Ata Social Media da Maliya Media Reporter na ƙaramar hukumar Gabasawa, Buhari Muhammad Karmami, ya karrama Ministan.

Ya ce sun karrama ƙaramin Ministan Gidaje, Hon. Yusuf Abdullahi Ata ne saboda tunda ake ministoci daga Kano ba a sami kamar sa a wajen taimakon jama’a ba.

Muhammad Karmami ya ce, Hon. Ata ya riƙe Ma’aikatar da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya ba shi da kulawa da yin aiki tuƙuru, tare da kawo cigaba.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum