Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Jagoran Kwankwasiya kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta samun wani sauyi a jerin ’yan takarar jam’iyyar a jihar Kano.
Kwankwaso ya ce dukkan ’yan takarar da aka tsayar a baya suna nan daram, yana mai cewa jam’iyyar ba ta san da wani sauyi da aka samu ba.
Ya bayyana mamakinsa kan yadda wani Sha’aban Sharada, wanda ya ce ɗan jam’iyyar APC ne, ke ikirarin cewa shi ma ɗan takarar jam’iyyar NDC ne.
“Iya fitina a kwance take. Ko da kuka ga muna zaune lafiya, ba ma shiga rigingimu da babu gaira babu dalili,” in ji Kwankwaso.
Ya ƙara da cewa: “Amma wannan ba ya hana ka, in kana tafiya, rigima ta taso maka. Amma dai in kana da gaskiya, Allah sai ya taimake ka. Mu ba ma yin gaba mu yi baya. Inda muka yi, ko da kuskure ne, nan muke tsayawa. Kuma kullum jama’a shigowa jam’iyyar NDC suke yi.”
A nasa ɓangaren, shugaban jam’iyyar NDC reshen jihar Kano, Hon. Husaini Isah Mairiga, ya tabbatar da cewa an samu sauyin sunayen ’yan takarar majalisar dokokin jihar guda biyar, inda ya ce ɗaya daga cikinsu ya janye, aka maye gurbinsa da wani, yayin da sauran huɗun sunayensu suke cikin kundin da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta fitar,6 wanda ya ce shi ne ingantaccen jerin sunayen.
Mairiga ya ce, a fahimtarsa, Jagora Dakta Rabiu Musa Kwankwaso na tare da jam’iyyar NDC, kuma yana mu’amala da shi kai tsaye a matsayinsa na shugaban jam’iyyar a Kano.
Ya ce jerin sunayen da INEC ta fitar na ’yan takarar majalisar dokokin jihar da na tarayya su ne halastattun ’yan takarar jam’iyyar. Ya ƙara da cewa a mazaɓar Birni, sunan Yusuf Kofar Mata ne ya fito a matsayin ɗan takarar majalisar tarayya.
Mairiga ya jaddada cewa: “Babu wani rikici a tsakaninmu a jam’iyya. Ina tare da Kwankwaso dari bisa dari. Jam’iyyun adawa ba abin da ba za su yi ba don su ga an samu matsaloli.”






