Daga Zubairu Lawal
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ya bayyana Zaben sabbin Shugabannin ta hanyar yarjejeniya a Jihar Nasarawa domin jagorantar harkokin jam’iyyar na tsawon shekaru huɗu masu zuwa.
A yayin babban taron jam’iyyar na jiha da aka gudanar a ranar Asabar a Lafia, wakilai daga dukkan ƙananan hukumomi 13 sun amince baki ɗaya da shugabancin, inda aka tabbatar da Hon. John Michael-Abdul a matsayin Shugaba.
A jawabinsa na karɓar aiki, Shugaban, Hon. Michael-Abdul ya ce zai himmatu wajen sauya fasalin ADC domin ta zama wata ƙaƙƙarfan madadin jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC).
Ya bayyana cewa kwamitin zartarwa na jihar zai mayar da hankali kan wayar da kai a matakin ƙasa (grassroots), tabbatar da dimokuraɗiyya cikin gida, da kuma gudanar da siyasa bisa muhimman batutuwa a lokacin yaƙin neman zaɓe.
Hon. Abdul, wanda tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa ne, ya nuna kwarin gwiwa cewa jam’iyyar za ta karɓi ragamar mulkin ƙasa da jihar daga hannun APC a shekarar 2027.
Ya ce manufar sabon kwamitin ita ce gina jam’iyya mai wakiltar gaskiya, haɗin kai, da kuma ingantaccen hidima ga al’ummar jihar.
“Yau, ta hanyar wannan yarjejeniya da wannan babban taro, kun ɗora mana alhakin yi wa babbar jam’iyyarmu hidima na tsawon shekaru huɗu masu zuwa, kuma mun karɓa cikin tawali’u da kuma ƙudurin sauke nauyin da aka ɗora mana.
ADC a Jihar Nasarawa babbar iyali ce mai manufa guda—ta bunƙasa jam’iyya, ta lashe zaɓe, tare da kawo ingantaccen shugabanci ga al’umma,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa cikin kwanaki 30 masu zuwa, kwamitin zai fitar da cikakken tsarin aiki domin ƙarfafa jam’iyyar a rumfunan zaɓe 147, ƙananan hukumomi 13 da kuma a matakin jiha baki ɗaya.
Shugaban Kwamitin Taron, Kani Jibarang, ya bayyana tsarin zaɓen a matsayin “mai cike da zaman lafiya da gaskiya.”
A nasa bangaren, tsohon Shugaban jam’iyyar, Barr. Paul Magaji, ya gode wa jam’iyyar bisa damar da aka ba shi na yin aiki, tare da kira ga mambobi da su bai wa sabon shugaba cikakken goyon baya.
Rahoton The Voice ya nuna cewa an rantsar da sabbin shugabannin nan take bayan amincewar wakilai, inda Barr. John Matthew ya jagoranci rantsuwar, lamarin da ya tabbatar da sauyin shugabanci cikin kwanciyar hankali a reshen jam’iyyar na jihar.







