Ku Guji Rikici Da Sunan Addini — Shaikh Zakzaky Ga Musulmi Da Kiristoci

Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya ja hankalin musulmi da kirista a fadin kasar nan da su guji abin da zai hada su fada da sunan addini ko kabilanci.

Shehin Malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin wakilan al’ummar Unguwar Nasarawa da ke Kaduna, a wata ziyara ta musamman da ta ƙunshi manyan shugabannin addinai daga ɓangarorin Musulmi da Kiristoci a ranar Talata a gidansa dake Abuja.

Cikin tawagar akwai Mista Zakari, wakilin ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) a ƙaramar hukumar Chikun, Alhaji Aliyu Mai Lafiya Chiroman Nasarawa, Mista Dominic, babban faston cocin Katolika na Unguwar Nasarawa, da Shaikh Alaramma Jabir Muhammad, babban limamin masallacin Juma’a na yankin.

A yayin ganawar wacce ta kasance a ranar Talata 4 ga watan Nuwamban 2025 wacce Ofishin Shehin Malamin ya labarta, Shaikh Zakzaky ya yi kira mai ƙarfi ga al’umma da su guji kowacce irin fitina ko rikici da za ta iya kawo rabuwar kai tsakanin Musulmi da Kiristoci.

Ya ce, “Kar ku yarda a haɗa ku rigima da juna, ko da da sunan addini ko da da sunan ƙabila. Ku zauna lafiya, ku haɗa kai domin amfanin kowa da kowa.”

Shehin Malamin ya bayyana cewa Kiristoci ba ‘arna’ ba ne, yana mai tunatar da cewa Allah Maɗaukaki ya ambace su a cikin Alƙur’ani da suna “Ma’abota Littafi”. Ya ce wannan dalili ne da ya wajabta a ci gaba da girmama juna da ƙarfafa zumunci da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinan.

Wannan ganawa ta kasance wata dama ta ƙarfafa haɗin kai da fahimtar juna a tsakanin shugabannin addinai a Nasarawa, abin da da dama suka yaba da shi a matsayin mataki mai muhimmanci wajen gina zaman lafiya da haɗin kai a Kaduna da ma kasar baki ɗaya.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo