Muna Nan Kan Cigaba Da Raya Sana’o’inmu Na Gargajiya Ƙaramar Hukumar Takai, Kano -Hon. Muktari Faruruwa

Daga Ibrahim Muhammad

Ƙaramar hukumar Takai ta jihar Kano na nan riƙe da al’adunta a fannin sana’ar saƙa ta kaba da ake yin tabarmin kaba da faifai da mafifitai da sauran abubuwa na gargajiya.

Shugaban ƙaramar hukumar Takai Hon. Muktari Ibrahim Faruruwa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a rumfar ƙaramar hukumar a yayin taron nuna al’adun gargajiya da gwamnatin jihar Kano ta gudanar.

Ya yi nuni da cewa a baya bisa al’ada duk wasu abubuwa ma tun daga na ajiye kayan sawa da na abinci da na cin abincin ma da na zama da na rufe kayayyaki duk mafi yawa da kaba ake saƙa su. “Don haka mu al’ummar Takai ba mu jefar da wannan sana’a ta tarihi ba. Muna tare da ita har yanzu,” in ji shi.

Hon. Muktar Ibrahim Faruruwa ya bayyana cewa su a ƙaramar hukumar Takai suna da kayayyaki na al’ada suna kuma noma sosai, suna kuma da dabino wanda da lokacin da ya yi ‘ya’ya ne ma da sun zo da shi wajen taron da aka yi na baje kolin kayayyakin al’adu na gargajiya.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum