Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa ta jihar Kano (AMATA) ta gudanar da taron saukar Alƙur’ani da addu’o’i na musamman domin neman kariya ga jihar da kasuwanninta, sakamakon yawaitar gobara, musamman wadda ta auku a Kasuwar Singa.
Shugaban AMATA na jihar, Alhaji Abdul’Aziz Ɗalha Musa, ya ce an shirya addu’o’in ne domin neman yafiya da kariyar Allah kan iftila’in gobarar da ta jawo asarar dukiya mai yawa. Ya ce an sauke Alƙur’ani sau 10, tare da zikiri da addu’o’i na musamman.
Dangane da gobarar Singa, Musa ya ce sun gamsu da yadda aka tantance ’yan kasuwar da abin ya shafa sama da 1,500, tare da haɗin gwiwar hukumomin NEMA da SEMA.

Ya ƙara da cewa suna sa ran tallafin da Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kano suka yi alƙawari zai isa ga waɗanda abin ya shafa.
Sai dai ya koka kan rashin wakilcin AMATA a kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gwamnati domin duba batun tallafin, duk da cewa a ofishin ƙungiyar ne aka gudanar da tantancewar.
Ya ce sun rubuta takarda ga Sakataren Gwamnati da Kwamishinan Yaɗa Labarai domin a duba lamarin, yana mai zaton Gwamnan ba shi da masaniya kan hakan.
Ya roƙi Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya sake duba tsarin kwamitin domin tabbatar da adalci da wakilcin da ya dace, yana mai jaddada cewa manufarsu ita ce rage raɗaɗin da ’yan kasuwa ke ciki.
A nasa jawabin, Sarkin Kasuwar Singa, Alhaji Isah Abba, ya ce addu’a ita ce mafita ga duk wani iftila’i, yana mai kira ga al’umma da su ƙara komawa ga Allah domin samun zaman lafiya da kariya.








