An Ɗage Dokar Hana Yin ‘Yan Achaɓa A Kwaryar Birnin Kano Ne?

Daga Ibrahim Muhammad

An ja hankalin hukumomin tsaro da gwamnatin jihar Kano a kan yadda aka lura harkar haya da babura masu ƙafa biyu da ake ce wa ‘yan Achaɓa na dawowa ana yi a cikin ƙwaryar Birnin Kano duk da cewa ba a sanar a hukumance an ɗage dokar hani da aka yi ba a shekarun baya saboda matsalar tsaro.

Malam Sa’idu Adamu ne ya yi wannan jan hankalin da yake zantawa da manema labarai, ya ƙara da cewa a baya ya lura ana ɗan yin hayan babur ɗin Achaɓan jefi-jefi ne a ‘yan keɓantattun wurare da suka haɗa da unguwanni Kurna, Rijiyar Lemo da Bachirawa, su ke ɗaukar fasinjoji su shigar da su lunguna saboda nisa. Daga baya kuma sai ake yi a yankin unguwannin Sabon Gari.

Ya ce yanzu kuma harkar ta Achaɓa tana daɗa ƙarfi ne har ta kai sun soma yin gungu-gungu a wurare suna taruwa musamman a cikin yankunan ƙananan hukumomin Fagge, Dala, Nasarawa da Birnin Kano, yanzu masu Achaɓar suna yawo neman fasinja a cikin gari da rana unguwa-unguwa suna haya har wasu ma suna shigowa da baburan daga wajen jihar Kano su yi.

Sa’idu Adamu ya yi nuni da cewa duk kai wa da kawowa da ake yi na haya da baburan da ya dawo ake yi gadan-gadan a Kano a tsakanin jama’a, ya lura suna yi ne a kan idanun jami’an tsaro, don haka yake ganin in aka yi duba da dalilai da suka sa aka hana Achaɓar a baya yin wasarere da aka yi da dawowar Achaɓar, ba ƙaramin sakaci ba ne daga gwamnatin Kano da hukumomin tsaro in aka yi la’akari abubuwa da suka faru a baya da yadda harkar tsaro ke cikin yanayi a yanzu.

Don haka ya ce yana kira ga hukumomin tsaro da gwamnatin jihar Kano ta duba wannan lamari na neman dawowar Achaɓa ta ɗauki mataki da ya kamata ko da ba za a hana ba, ya zama an san masu yi ana kula da su domin kar sai abu ya yi ƙarfi sosai ko wani abu mara daɗi ya auku (Allah ya kiyaye), kar a zo a yi fargar Jaji.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo