An Cimma Kashi 85 Na Aikin Sabon Ginin Kasuwar Jawwala -’Yan Kasuwa Sun Yaba Wa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Sakataren Kasuwar Waya ta Jawwala da ke Kofar Mata a Kano, Musa Balarabe, ya bayyana cewa aikin ginin sabon kasuwar na zamani ya kai kashi 85 cikin 100 na kammalawa.

Musa Balarabe ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano, inda ya ce aikin yana tafiya cikin sauri da nasara.

A cewarsa, a halin yanzu ana aikin hawa na uku, wanda shi ne mataki na ƙarshe na ginin, kuma har an fara aikin filasta a wasu sassa na ginin.

Ya ce an kammala gina shaguna da banɗakuna a bene na ƙasa, sannan an kammala hawa na farko da na biyu.

Ya ƙara da cewa hawa na biyu ya ƙunshi babban masallaci da ƙarin shaguna domin amfanin ’yan kasuwa.
“Yanzu haka ana aikin hawa na uku, kuma nan ba da jimawa ba za a kammala aikin domin ’yan kasuwa su ci gaba da harkokinsu cikin sabon ginin,” in ji shi.

Musa Balarabe ya ce Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ce ta bayar da aikin domin faɗaɗa kasuwar Jawwala, wacce ya ce ta zama cibiyar sana’ar waya da ke ɗauke da dubban matasa masu saye da sayarwa.

Ya bayyana cewa faɗaɗa kasuwar zai taimaka wajen rage zaman banza da rashin aikin yi a tsakanin matasa.

Ya tunatar da cewa kafin kafa kasuwar Jawwala, ana kiran yankin da sunayen “Hauren Balagu” da “Hauren Joka”, inda ya ce mutane da dama kan kauce wa zuwa wurin saboda yawan matasan da ke zaman banza.

A cewarsa, a lokacin mulkin tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, aka yanke shawarar mayar da yankin kasuwa domin bai wa matasa damar koyon sana’a da dogaro da kai.

“Tun bayan kafa kasuwar, matasa da dama sun koyi sana’ar waya, sun samu aikin yi, kuma sun daina wasu halaye marasa kyau,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa zuwan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙara wa kasuwar tagomashi, inda ya ga muhimmancin faɗaɗa ta domin ta ɗauki ƙarin mutane masu gudanar da sana’o’i.

“A baya kasuwar tana ɗaukar kusan mutum 1,000 ne, amma da wannan sabon ginin ana sa ran za ta iya ɗaukar sama da mutum 10,000 masu gudanar da harkokin kasuwanci,” ya bayyana.

Musa Balarabe ya ce mafi yawan ’yan kasuwar ’yan asalin Jihar Kano ne daga unguwannin da ke kewaye da kasuwar, saboda haka suna yabawa gwamnatin jihar bisa irin tallafin da take ba su.

Ya ce ’yan kasuwar na ci gaba da yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf addu’ar samun nasara da kuma damar ci gaba da mulki domin kammala ayyukan ci gaba da ya fara.

Har ila yau, ya ce idan aka kammala aikin ginin kasuwar, ’yan kasuwar za su mara wa gwamnan baya wajen wayar da kan jama’a kan irin ci gaban da gwamnatin ta kawo musu.

Sakataren kasuwar ya kuma yaba wa Shugaban Kasuwar Jawwala, Hon. Kamal Yusha’u Mai Jawwala, bisa tsarin da ya bullo da shi na gudanar da aikin ginin ba tare da rusa dukkan kasuwar lokaci guda ba.

Ya ce an fara gina sabon sashen kasuwar ne domin bai wa ’yan kasuwa damar ci gaba da gudanar da sana’arsu kafin daga bisani a rushe tsoffin sassan domin a gyara su a matakai.

“Aikin yana tafiya ne mataki-mataki ba tare da an dakatar da kowa daga sana’arsa ba,” in ji shi.

Musa Balarabe ya ce duk wani ci gaba da ake samu a kasuwar na da nasaba da goyon bayan gwamnatin jihar, yana mai cewa yanzu shagunan da za a rabawa ’yan kasuwa za su kasance mallakinsu ne kai tsaye.

Ya yi kira ga ’yan kasuwar Jawwala da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da bai wa gwamnati haɗin kai, ganin yadda aikin ke tafiya yadda ya kamata.

A ƙarshe, ya bayyana cewa Kasuwar Waya ta Farm Centre ce kaɗai take gaba da Jawwala a Kano, yana mai cewa kasuwar Jawwala na daga cikin manyan kasuwannin waya mallakin ’yan asalin jihar Kano da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ke ƙara faɗaɗawa domin bunƙasa harkokin kasuwanci a jihar.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum