Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta jihar Kano ta jagoranci wasu ‘yan mata uku masu sana’ar gala zuwa ga karɓar addinin Musulunci, bayan sun bayyana aniyarsu ta rungumar addinin.
An gudanar da taron ne a harabar ɗakin taro na hukumar, cikin wani yanayi na farin ciki da murna.
Shugaban Hukumar, Abba El-Mustapha, ne ya jagoranci ‘yan matan wajen karɓar addinin Musulunci tare da yi musu addu’o’i da fatan alheri.
Da yake jawabi a wajen taron, Abba El-Mustapha ya bayyana ranar a matsayin ɗaya daga cikin ranakun farin ciki a rayuwarsa.
Ya ce shawarar da ‘yan matan suka yanke ta samo asali ne daga kyawawan halaye da mu’amala irin ta Musulmai da suka gani daga abokan sana’arsu da kawayensu a masana’antar nishaɗi.
‘Yan matan ukun, waɗanda aka bayyana sunayensu da Dicson da Zara daga jihar Adamawa, sai kuma Hannatu daga Jihar Gombe, sun ce sun shafe lokaci suna gudanar da sana’ar gala a Kano kafin yanke shawarar rungumar addinin Musulunci.
Sun bayyana farin cikinsu kan matakin da suka ɗauka, tare da godewa al’ummar Kano bisa irin soyayya, zaman lafiya da kyakkyawar mu’amala da suka nuna musu.
Da take magana a madadin waɗanda suka karɓi Musulunci, Hannatu ta ce kyawawan koyarwar addinin Musulunci da yadda Musulmi ke rayuwa cikin zaman lafiya da taimakon juna ne suka ja hankalinsu zuwa ga rungumar addinin.
Ta ce sun gamsu da irin tarbiyya da kyawawan halaye da suka gani daga abokansu Musulmi, wanda hakan ya ƙarfafa musu guiwar ɗaukar wannan mataki.
Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da ba sabbin Musulman goyon baya tare da koya musu muhimman darussa na addini domin su samu cikakkiyar fahimta da kuma tsayawa daram a kan sabon tafarkin da suka fara.







