Daga Ibrahim Muhammad Kano
An fara gudanar da bikin cikar Kwalejin Shari’a da Nazarin Addinin Musulunci ta Aminu Kano (AKCILS) shekaru 50 da kafuwa, a wannan rana ta Litinin a jihar Kano.
An fara taron ne da addu’o’i na musamman da aka gudanar a babban masallacin harabar Kwalejin da safe. Sannan daga bisani aka gudanar da taron jawabai a ɗaya daga cikin zauren tarukan makarantar, inda malamai suka gabatar da jawabai kan batutuwa daban-daban.
Da yake zantawa da manema labarai, shugaban Kwalejin, Farfesa Balarabe Jakada, ya ce maƙasudin taron shi ne haɗa shugabannin makarantar na yanzu da ma’aikata, ɗalibai, da tsofaffin ɗaliban da Allah Ya yi wa albarka suka kai matakai daban-daban, domin su yi wa Allah godiya kan cikar kwalejin shekaru 50 da kafuwa.
Ya ce taron zai duba irin nasarorin da aka samu a tsawon shekarun da suka gabata, da kuma ƙalubalen da makarantar ke fuskanta.
“A yau Litinin da ƙarfe 9 na safe muka fara taron da addu’o’i a babban masallacin Kwalejin da aka gyara aka kawata.
Manyan malamai, alarammomi, hafizai da gwanayen Alƙur’ani sun yi sauka tare da addu’o’i ga Kwalejin, jihar Kano da kuma kasa baki ɗaya, domin Allah ya zaunar mana da ƙasa lafiya, ya kuma yi jagora ga shugabanninmu,” in ji shi.
Farfesa Jakada ya bayyana cewa shi ne shugaban Kwalejin da ya fi daɗewa a kan kujerar shugabanci, inda ya kusa cika shekaru takwas, yana mai cewa wannan dama da ya samu al’amari ne na Allah, kuma suna godiya gare Shi bisa wannan ni’ima.
Ya kuma gode wa tsohon Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya naɗa shi a karo na farko, tare da yaba wa Gwamnan jihar Kano na yanzu, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa ba shi damar ci gaba da aikinsa da kuma tallafin da yake ba Kwalejin.
Ya ce taron da aka fara a ranar Litinin, 27 ga Afrilu, 2026, zai gudana na tsawon kwanaki uku, inda ake sa ran Gwamna Abba Kabir Yusuf da Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, za su halarci bikin rufe taron, inda Sarkin Kano zai kasance uban taro.
Game da nasarorin da Kwalejin ta samu a ƙarƙashin jagorancinsa, Farfesa Jakada ya ce duk wanda ya san makarantar tun kafin zuwansa zai ga babban sauyi a bangarorin walwala da ci gaban makarantar.
Ya ce an ƙara sabbin darussa, an buɗe sababbin sassa, kuma an inganta gine-gine da yanayin makarantar, har ta kai ga wasu idan suka zo suna ɗaukar cewa jami’a ce.
Ya ƙara da cewa daga cikin manyan nasarorin da aka samu akwai fara shirye-shiryen karatun digiri tare da haɗin gwiwar Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-Ma, da kuma samun amincewar National Board for Technical Education (NBTE) da JAMB, wanda ya sa diplomomin da Kwalejin ke bayarwa suka zama na ƙasa.








