Ba Za Mu Zura Ido Ana Haike Wa Darajar Manzon Allah Ba -Ƙaramin Ministan Gidaje A Rabon Tallafin Ga Sha’irai 500

Daga Ibrahim Muhammad Kano

A bayyana cewa Kano Allah ya kafa ta ne a kan abubuwa uku, addinin Musulunci, kasuwanci da ƙasaitar masarautarta, shi ya sa yaro ɗan asalin Kano komai rashin jin sa da sakacinsa ga addini idan ka taɓa addini sai ya nemi ya mutu a kan wannan.

Haka yaran aka taso da su. Haka garin yake da alkhairi. Haka ake tafiya a kai.

Ƙaramin Ministan Gidaje, Hon. Yusuf Abdullahi Ata ne ya bayyana hakan cikin jawabinsa a taron da ya gudanar na tallafawa mawaƙa masu yabon Manzon Allah Sha’irai a Kano a yammacin ranar Asabar a ɗakin taro na Mambayya.

Ya ƙara da bayanin cewa, sai kuma kasuwanci da Allah ya albarkaci Kano da ita da kuma kimar masarautar ta, da a duk duniya har masarautar Ingila ta san masarautar Kano na daga cikin mai daraja na ɗaya.

Sai dai Ministan Yusuf Abdullahi Ata ya ce waɗannan abubuwa uku da Allah ya yi wa Kano daraja da su a yanzu, kuma sun shiga a uku a Kanon.

“Harkar addinin da kasuwanci da masarauta duk sun shiga a uku. Akwai buƙatar mu natsu a haɗa kai a zaɓi shugabanci da ya dace da garin yadda Allah zai sake kallon mu da jinkansa,” in ji shi.

Ya koka da cewa, “Yanzu abubuwa da suke fitowa na kalamai marasa daɗi in ban da alfarmar garin, da Allah ya yi mana tsanani fiye da abin da ya faru a Maiduguri, amma an yi sa’a da yake iyaye da kakanni sun nemi alfarma a kan garin Kano da irin soyayya da ake yi wa Annabi (SAW), shi ya sa Allah yake sauƙaƙa mana. Akwai buƙatar a sami ingantacciyar gwamnati da za ta riƙa tsawatarwa duk wanda ya haikewa darajar Manzon Allah (SAW) a ɗauki mataki na hukunci a kansa. Wannan shi ne matsayinmu,” cewar ƙaramin Ministan Gidajen.

Hon. Yusuf Abdullahi Ata ya ƙara da cewa, “Duk sanda muka sami dama wannan shaƙiyancin ba wanda zai mana daraja ko wace iri ce, ba ta Annabi (SAW) kaɗai ba, ba ta tsira sai an ɗauki matakin da ya kamata, amma ba za mu zo muna zaune a riƙa kawo mana masifa kala-kala ba, ko a sami wani mai da’awar malanta ko ta siyasa a riƙa abin da aka ga dama ba. Ba za mu yarda da haka ba”

Ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da cewa, “Dole ne a dage ‘yan majalisa na jiha da na tarayya da sauran shugabanni a riƙa zaɓen mutanen kirki nagartattu da za su riƙe amana, amma ba a bar abu barkatai ba, mutanen da gidajensu ma ba za su iya riƙewa ba, a ce sune shugabanni, amma an zuba ido. Dole ne a fito a faɗakar da mutanen Kano da mafi yawansu na kirki ne a kan zaɓar shugabanni na kirki.”

Hon. Yusuf Abdullahi Ata ya bayyana cewa irin waɗannan tarurruka na rabon tallafi kamar yadda aka sani su a wurin su tun lokacin da suka soma siyasa, an kawo su siyasa ne domin yin irin waɗannan hidima da ta shafi addinin musulunci. Rana ɗaya aka ce su shiga siyasa har malamansu da iyaye kowa ya ce ba su dace ba sai da aka kai aka kawo sannan aka ba da izni aka shiga.

Ya ce tunda suka shiga harkar siyasa har yau ba su zame a kan addini ba, ba su yarda su rabu da al’ummarsu ko malamansu ba. Ko saboda wata siyasa, ba su rabu da makarantun addini da suke jagoranci ba. Ko a baya ma shekaru da suka gabata da ya halarci Maulidi da Hajiya Fatima Dala shugabar mata ta APC ta shirya a nan ma ya taɓa bayar da kujerun Umara ga masu yabon Annabi sun je tare da su ziyarar Annabi, kuma yana gode wa Allah har yanzu yana tawassali da irin waɗannan ayyuka da sune suke tafi da su.

Hon. Ata ya ce ko wannan muƙami da ya samu na Minista duk wanda ya san shi, ba cas ba as, in dai a harkar siyasa ce, domin shekara biyar ma ba ya cikin harkar, yana zaune, da mai naɗawan ya yi ikon sa, aka kira su aka ce zo a tafi. “Saboda haka ba za mu rabu da irin waɗnnan ayyukan ba,” in ji shi.

Ƙaramin Ministan Gidajen na Nijeriya, Hon. Yusuf Abdullahi Ata ya ce sun fara irin wannan tallafin ne da Limamai da Ladanai da Na’ibai na masallatan Juma’a guda 540 a jihar Kano mutum 1,620 ne suka amfana da kayan abinci da tallafi na kuɗi bayan nasu an yi na ‘yan Social Media na Kano. Sannan suka kira masu buƙata ta musamman su 500 har zuwa yanzu da aka zo kan masu yabon Annabi da aka bai wa Sha’irai 500 tallafin kuɗi. Nan gaba za a yi wa alarammomi da marayu.

  • Related Posts

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2027 mai kimanin Naira Tiriliyan 1.107 ga Majalisar Dokokin jihar Kano, inda ya…

    Takarar Majalisar Jaha Da Nake A ADP Amsa Kiran Al’ummar Gwale Ne -Dakta Bashir Aliyu Galadanci

    Dag Ibrahim Muhammad Kano Dan takarar majalisar dokokin Jihar Kano a Karamar Hukumar Gwale a jam’iyyar ADP, Dakta Bashir Aliyu Galadanci, ya bayyana cewa al’ummar karamar hukumar ne suka matsa…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum