Babu Sauran Cire-Ciren Kudin Da Ba Sa Bisa Ka’ida A Albashi Ma’aikatan Zamfara

Gwamna Lawal Ya Haramta Cire-ciren Kuɗi Ba Bisa Ƙa’ida Ba Daga Albashin Ma’aikatan ZamfaraGwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umurnin dakatar da duk wani nau’in cirar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba daga albashin ma’aikatan jihar.Wannan ya biyo bayan da Ma’aikatan Zamfara suk koka tare da ƙorafe-ƙorafe da dama dangane cire-ciren kuɗi da ake yi musu a tsarin biyan albashin jihar.A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar a Gusau, ya bayyana cewa umurnin da aka bayar ya haramta duk wani nau’in cirar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba da ake yi ta hanyar biyan albashin gwamnatin Jihar Zamfara.Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A cikin ƙudirinsa na tsaftace tsarin biyan albashin ma’aikatan jihar Zamfara don samun ingantaccen tsarin biyan albashin su a adaidai lokacin da suke fuskantar cire-ciren kuɗi ba bisa ƙa’ida ba, Gwamna Dauda Lawal ya bayar da umarnin dakatar da duk wasu bangarori da ba sa bin doka da oda wajen zaftare wani sashi daga albashin ma’aikata.“An yanke hukuncin ne saboda ƙorafe-ƙorafen da ake yi na cire-ciren kuɗi daga albashin ma’aikata, inda ake zaftare wasu kuɗaɗen da sunan wasu ƙungiyoyin haɗin gwiwa na ‘Cooperatives’, wasu kuma da sunan biyan wasu basukan kayayyaki.“Gwamna Lawal ya umurci kwamishinan kuɗi da ya dakatar da duk irin wannan cire-cire daga albashin ma’aikata tare da isar da umarnin ga duk ƙungiyoyin haɗin gwiwa da sauran masu sayar da kayayyaki.”Don ƙarin haske, bangarorin da aka yarda kaɗai su cire kuɗi su ne: PAYE; Kuɗin ƙungiya; NHF; ZAMCHEMA; kuɗin amfani da ruwa; FMB (Hayar Gida kafin Mallaka); FMB (Gyarar Gida); Kuɗin hannun jari.“Gwamnatin da ke yanzu a jihar Zamfara ta himmatu wajen aiwatar da matakan da za su taimaka wa walwala da ci gaban ma’aikatan ta. Wannan ya haɗa da haɓaka yanayin aiki, samar da albarkatun da suka dace, da kuma samar da yanayi mai kyau don tabbatar da ƙwararewar ma’aikata wajen gudanar da ayyukan su.

Related Posts

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum