
Daga Ibrahim Muhammad Kano
An yi kira ga al’ummar Kano da ƙasar nan su yi karatun ta-natsu su sake jarraba jam’iyyar PDP domin za ta dawo musu da walwala da sauƙin rayuwa, su ɗauke su daga inda APC ta ajiye su yanzu su mayar da su tashar da suka bar su cikin walwala da sauƙin rayuwa a baya, amma APC ta ɗauko su ta jefa su a mawuyacin hali.
Sabon Mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na shiryar Kano ta tsakiya, Alhaji Kabiru Bello Ɗandago ne ya yi wannan kiran ne a wani taro na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar. Ya ce a shekara ta 2015 sai da suka gargaɗi jama’a da cewa, kar a kori jam’iyyar PDP domin sun san abin da ta tsara, amma mutanen Nijeriya suka ƙyeƙasa ƙasa suka ƙi, saboda yaudarar da aka yi musu.
Ya ce yanzu kowa ya duba aljihunsa da tukunyarsa, mace ta gaya wa mijinta irin ƙunci na halin rayuwa na zamantakewa da suke gani tun daga 2015 da jam’iyyar PDP ta bar gwamnati zuwa yanzu.
Ya ce a lokacin mulkin gwamnatin PDP ana sayar da buhun shinkafa N8,000, amma yanzu fa? Kwanon shinkafa ya gagari talakawa.
Alhaji Kabiru Bello Ɗandago ya ce a matsayinsa na mataimakin shugaban jam’iyyar PDP a shiryar Kano ta tsakiya yadda aka gudanar da zaɓe aka gama lafiya babbar nasara ce a gare su a jam’iyyar.
Don haka ya ja hankalin ‘yan jam’iyyar PDP su sani jam’iyyar tasu ba ta shugabanni ba ce kaɗai, ta duk ‘ya’yan jam’iyyar ne, da sauran duk wanda ya amince da ita. Hatta mai zaɓe in ya yarda da ita yana iya zama mai ruwa da tsaki a cikinta.
Alhaji Kabiru Bello Ɗandago ya ce zai gabatar da ayyukan da za su zama na samun ci gaba ga jam’iyyar a jihar Kano.
“Zaɓen fitar da shugabannin jam’iyyar da aka gudanar ya yi wa wasu daɗi, wasu kuma akasin haka, amma mu a matsayinmu na sabbin shugabanni aikinmu na farko shi ne mu yi rarrashi da bayar da haƙuri da saka ci gaban jam’iyyar a gaba,” in ji shi.







